
Jagororin ƙasa na tafiyar Kwankwasiyya sun gudanar da wata ganawa ta musamman da jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa, Henry Seriake Dickson, tare da sauran shugabannin jam’iyyar domin tattauna matsalolin da suka kunno kai tsakanin tafiyar Kwankwasiyya da wasu tsoffin shugabannin NDC a Jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Barrista Osa Director, ya fitar, an bayyana cewa an gudanar da taron ne a cikin sirri, inda shugabannin NDC suka yi sasanci da nufin samar da haɗin kai da tabbatar da bai wa kowane ɗan jam’iyya damar shiga cikin harkokin jam’iyyar.
Sanarwar ta ce shugabancin NDC ba zai tilasta zaɓen ’yan takara a Jihar Kano ko a sauran jihohin ƙasar nan ba, yana mai jaddada cewa jam’iyyar na mutunta tsarin dimokuraɗiyyar cikin gida wajen zaɓen ’yan takararta.
An kuma bayyana cewa taron, wanda ya ɗauki sa’o’i da dama, ya kasance mai amfani tare da samar da kyakkyawar fahimta tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa har yanzu ba ta fitar da wani sakamako na hukuma dangane da zaɓukan fidda gwani a kowace jiha ba, tare da yin kira ga mambobi da sauran jama’a da su yi watsi da duk wata jerin sunaye ko sakamakon zaɓe da ake yaɗawa a halin yanzu, domin ba na hukuma ba ne.
