Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gidauniyar IMRAJ Hope Foundation tare da haɗin gwiwar ma’aikatar matasa ta Jihar Katsina sun gudanar da taron tattaunawa na matasa mai taken “matasa cikin jagoranci da shiga harkokin siyasa”, domin wayar da kan matasa kan muhimmancin shiga harkokin siyasa da jagoranci tare da taka rawar gani wajen ci gaban al’umma.
Taron ƙarƙashin jagorancin Hajiya Rabi’atu Jalli ta shirya taron domin wayar da kan matasa tare da tattaunawa kan shigar matasa cikin harkokin jagoranci da siyasa.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron, shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir Andaje, ya bayyana matasa a matsayin ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Ya buƙace su da su kasance masu kishin ƙasa, bin doka da oda, tare da neman ilimi da ƙwarewa domin su zama shugabanni nagari da za su jagoranci al’umma a nan gaba.
A nata jawabin, Shugabar Gidauniyar IMRAJ Hope Foundation, Hajiya Rabi’atu Jalli, ta ce an shirya taron ne domin ƙara wayar da matasa kan muhimmancin shiga harkokin siyasa da shugabanci.
Ta bayyana cewa gidauniyar za ta ci gaba da shirya irin waɗannan taruka da shirye-shirye domin bunƙasa rayuwar matasa da ƙarfafa musu gwiwa wajen bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.
Shi ma mai bai wa gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin matasa, Alhaji Nasiru Ahmad Lara, ya yi kira ga matasa da su yi amfani da damar da suke da ita wajen shiga harkokin siyasa da shugabanci cikin hikima da nagarta. Ya ce matasa na da muhimmiyar rawa wajen gina dimokuraɗiyya da tabbatar da ci gaban ƙasa.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Alhaji Isah Miqdad Saude, ya jaddada ƙudirin ƙaramar hukumar na ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke bunƙasa rayuwar matasa. Ya kuma buƙace su da su kasance masu haɗin kai, zaman lafiya da jajircewa wajen neman ilimi da shiga ayyukan raya ƙasa.
A yayin taron, Dakta Samir Halliru Mashi da Alhaji Khaleel Ibrahim sun gabatar da ƙasidu kan hanyoyi da tsare-tsaren da za su taimaka wajen ƙara shigar matasa cikin harkokin siyasa da jagoranci. Sun yi bayani kan muhimmancin ilimi, ƙwarewa, jajircewa da kuma shiga ƙungiyoyi da harkokin siyasa domin samun damar bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.
Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da babban sakataren ofishin majalisar zartarwa ta Jiha (Cabinet Office), kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa na jihar , Alhaji Mannir Ayuba Sulluɓawa, shugaban hukumar Hisbah, daraktocin ma’aikatar matasa, mai taimakawa gwamna kan harkokin matasa, Alhaji Muhammad Nuhu Nagaske, shugabannin ƙungiyoyin matasa daban-daban da kuma dimbin matasa maza da mata daga sassa daban-daban na jihar.
