
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An tabbatar da rasuwar fasinjoji guda uku bayan wata gocewa da jirgin ƙasa na Warri zuwa Itakpe ya yi.
Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne a ranar Litinin, wanda ya sa hukumomi suka gaggauta kai agaji da kuma fargabar rashin aminci a fannin sufurin jiragen ƙasa na Nijeriya.
Da take tabbatar da faruwar al’amarin, Hukumar Kula da Tashoshin jiragen ƙasa ta Ƙasa (NRC), ta ce tawagar bayar da agajin gaggawa sun je wajen da abin ya faru domin agaza wa waɗanda al’amarin ya shafa.
NRC ta kuma ce, tana kula da ci-gaban da ake samu kuma za ta bada ƙarin bayani akan al’amarin a lokacin da ya dace.
Hakan na zuwa ne ƙasa da wata guda da NRC ta dakatar da ayyuka a layin Warri zuwa Itakpe bayan shawarwarin gudanarwa da injiniyoyi suka bayar.
A lokacin ne hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne domin tabbatar gudanar da harkokin tashar bisa inganci da tsaron lafiyar fasinjoji.
