Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wani bom da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dasa a kan titin Bagege- zuwa Anka a jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da jikkata wasu, lamarin da ya jefa al’ummomin da ke kan hanyar cikin ruɗani.
Shaidu da majiyoyin yankin sun ce fashewar ta faru ne yayin da matafiya ke tafiya zuwa yankin ƙaramar hukumar Anka a yau Talata.
Hanyar, wacce ta haɗa ƙauyuka da dama da garin Anka, an daɗe ana sanya mata alama a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin da ke kawo cikas a jihar saboda yawan hare-haren ‘yan ta’adda da garkuwa da mutane.
Shaidu sun ce, na’urar ta fashe yayin da motoci ke tafiya a kan titin Bagege-Anka.
“Ƙarfin fashewar ya lalata motar kuma ya haifar da asarar rayuka nan take”.
Duk da cewa hukumomi ba su tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba tukuna, mazauna yankin sun ba da rahoton mutuwar mutane da dama.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa cibiyoyar lafiya da ke ƙaramar hukumar Anka don neman magani.
Al’ummar yankin sun yi imanin cewa ‘yan ta’adda da ke aiki a dazuzzukan da ke kewaye da Anka, Bagege, da Dansadau sune suka dasa na’urar fashewa mai suna IED.
Dabarar amfani da bama-bamai a kan hanyoyin karkara ta ƙaru a Zamfara da jihohin da ke maƙwabtaka da ita yayin da matsin lamba da jami’an tsaron yankin ke ƙaruwa.
Ayyukan kasuwanci a garin Anka sun ragu yayin da mazauna ke jimamin waɗanda aka kashe.
Shekaru da yawa, mazauna ƙaramar hukumar Anka sun rayu da barazanar sace sacen ‘yan ta’adda, satar shanu, da hare-haren kan hanya.
Amfani da bama bamai a kan babbar hanyar karkara ya haifar da fargaba game da ‘yancin zirga-zirga ga manoma, ‘yan kasuwa, da ɗalibai.
Rahotanni sun nuna cewar dazuzzuka kamar Muntsira, Sububu, da sauran su sun kasance maɓoya ga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Hukumomin tsaro, ciki har da sojoji, ‘yan sanda, da sabbin masu kare al’umma na Zamfara CPG, suna gudanar da ayyuka don share dazuzzukan tare da kakkaɓe duk wasu yan ta’adda a maboyar su.
Hanyar Bagege-Anka muhimmiyar hanya ce ga manoma da ke kai amfanin gona zuwa kasuwanni.
Kowane hari yana kawo cikas ga noma kuma yana ƙara tsananta rashin tsaron abinci a yankin.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa al’ummomin Zamfara suna sa ido sosai kan tsarin Jihar Kaduna na horar da masu gadin daji 1,000, suna fatan samun irin wannan matakin gaggawa daga gwamnatin Jihar.
“Hukumomin tsaro suna can a wurin da fashewar ta faru, kwashe waɗanda suka ji rauni, da kuma gano asalin IED ɗin”. Mazaunin ya ce
“Titin Bagege-Anka da sauran hanyoyin karkara suna buƙatar yin aikin share fage akai-akai don IEDs da kuma ƙara yawan sintiri. Jiragen sama marasa matuƙa na iya taimakawa wajen gano ayyukan dasa ababen fashewar a kan hanyoyin mu” . Inji wani mazaunin yankin
“Bayan tsaro, iyalan da suka rasa ‘yan uwansu za su buƙaci diyya, tallafin likita ga waɗanda suka ji rauni, da kuma kula da lafiyar su.”
“Wannan fashewar bom gari ne kai tsaye ga talakawan yankin da ke ƙoƙarin noma, kasuwanci, da rayuwa cikin kwanciyar hankali”. Mazaunin yankin ya ce
Mazaunin ya yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da Gwamnatin Tarayya da su ɗauki hare-haren IED a kan hanyoyin karkara a matsayin aikin gaggawa ta ƙasa.
“Muna kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da gwamnatin tarayya da su kawo karshen harin IED don bai wa manoma damar tafiya daga Bagege zuwa Anka ba tare da tsoron bama-bamai ba”. A cewar mazaunin yankin
