Akan satar ‘yan makaranta: Ina aka kwana?

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Zuciyata na cike da ƙunci da takaici dangane da halin da ƙasar mu ke ciki na jimamin satar yara ’yan makaranta da malamai a Jihar Oyo, bayan garkuwa da aka yi da wasu ‘yan makaranta da har yanzu suke hannun ’yan ta’adda a wata makaranta a Jihar Borno.

Ga wanda bai sani ba ko ba shi da cikakken labarin abin da ya faru. A wata ranar Jumma’a ta 15 ga watan Mayu ne dai wasu ’yan bindiga suka sace ɗalibai ’yan firamare 39 ciki har da ɗan shekara biyu da haihuwa da malamansu guda 7 daga wasu makarantun da ke garin Ahoro-Esinele a Jihar Oyo. Kuma tun daga sannan har kawo lokacin da nake wannan rubutu ba a samu damar ceto su ba, ko daidaita batun kuɗin da za a bayar a fanshe su.

Idan ba a manta ba, a irin wannan rana ne ta Jumma’a 15 ga watan Mayu wasu da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne a Jihar Borno suka yi garkuwa da ɗalibai guda 50 daga wata makarantar firamare ta Mussa a ƙaramar Hukumar Askira-Uba, waɗanda har kawo yanzu babu bayani dangane da makomar su, kuma babu wani hoɓɓasa da ake yi wajen nemo su.

Sai dai ba haka abin yake ba dangane da ɗaliban Jihar Oyo, yayin da hankalin gwamnati, da jami’an tsaro, da ƙungiyoyin ’yan gwagwarmaya ya karkata kan batun neman ɗalibai da malaman da ke hannun ’yan bindiga. Ba tare da la’akari da halin da sauran ɗaliban da aka sace a ɓangaren Arewa ke ciki ba. Ko kuma yadda wasu ’yan gwagwarmaya daga ɓangaren Arewa ke tunanin gwamnati ta yi watsi da su.

Kodayake mai magana da yawun bakin Shugaban ƙasa, Abdul’Aziz Abdul’Aziz, ya shaidawa tashar BBC Hausa cewa, saɓanin abubuwan da ake yaɗawa a zaurukan sada zumunta cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya fi nuna damuwa kan satar ýan makarantar da aka yi a Oyo, haƙiƙa ba gaskiya ba ne, domin a cewarsa Gwamnatin Tarayya ta damu matuƙa da halin taɓarɓarewar tsaro da ke faruwa a sassan ƙasar nan, musamman yadda yake shafar harkar ilimi, da rayuwar yara ƙanana.

A kowanne ɓangare, a cewarsa an samar da rundunonin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an tsaron dazuka da aka bai wa horo na musamman kan yaƙi da ’yan bindiga da ke fakewa cikin dazuka suna aikata ɓarna. Kuma an yi haka ne ba tare da nuna fifiko ga wani ɓangare na al’ummar ƙasar nan ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban ƙasa ya kuma bayar da umarnin a tura da wasu ƙarin jami’ai na musamman da aka bai wa horo kan sabbin dabarun yaƙi da ’yan ta’adda, domin ƙara tsananta bincike wajen aikin ceto waɗannan ɗalibai da malamansu. Bayan isar wata babbar tawaga ta manyan jami’an gwamnati da ke ƙarƙashin Babban Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da Ministan Tsaro, Christopher Musa, da Babban Sifeton ’Yan sanda, Tunji Disu, domin jajetawa jama’ar yankin kan mummunan al’amarin da ya faru.

Babu shakka, ba ma ɓangaren gwamnati ba, hatta a ɓangaren ’yan jarida da ’yan gwagwarmayar kare haƙƙoƙin ɗan adam, damuwar da aka nuna da kulawar da ake bai wa waɗannan ɗalibai da malamai na Jihar Oyo, ba a nuna kwatankwacin irin sa ba a lokacin da aka sace ‘yan makaranta a Kwara, inda aka sace fiye da ’yan makaranta 300 a Zamfara, Kebbi, Katsina, Neja, Borno da Yobe.

Bincike ya nuna cewa, tun a shekarar 2014 da aka sace ’yan matan Chibok 276, an sace ko an yi garkuwa da ɗalibai fiye da 2,500 daga makarantu 31, waɗanda kuma akasarin su daga jihohin Arewa ne. Idan ka ɗauke batun su ’yan matan Chibok da lamarin sace su ya ɗauki hankalin duniya sosai, babu wani lokaci da aka kalli batun garkuwa da ’yan makaranta da muhimmanci kamar a wannan karon. Shin me ya kawo haka? Ko don su ba daga Arewa suke ba? Ko kuwa akwai wani bambanci ne tsakanin ɗaliban Kudu da na Arewa?

A ganina dai dukkan waɗannan yara ’yan Nijeriya ne, iyaye ne suka haife su, kuma dukkansu abin da ya same su ya faru ne suna kan turbar neman ilimi, kuma babu wani bambanci a tsakaninsu, maza ne ko mata? Bai kamata gwamnati ta bayar da wata ƙofa da za a fahimci kamar tana nuna wa wani ɓangare wariya ko son kai kan harkar tsaro ko wani abu da yake haƙƙin ta ne ta kare su ba. Mun sani tana iya nata ƙoƙarin, kuma jami’anta na soji da ’yan sanda su ma suna nasu ƙoƙarin, amma gaskiya za mu iya cewa abin da suke yi ɗin bai wadatar ba.

Yayin da iyayen yara da malamai ke gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin daɗi da gazawar gwamnati kan shaanin tsaro, da rufe makarantu da ƙungiyoyin malamai suka yi, domin gwamnati ta saurari kukansu, muna fata idan gwamnati ta tashi motsawa ba ɗaliban Jihar Oyo kawai za a kuɓutar ba, har ma da na sauran jihohin Arewa da ake cigaba da yin cigaba da garkuwa da su.

By ukarofi

Leave a Reply