
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Tsaro DHQ, ta yi watsi da wani faifan bidiyon bogi da ya karaɗe kafafen sada zumunta da ke nuna Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Olufemi Oluyede da kuma wani a matsayin Shugaban Rundunar Sojoji (COAS), Laftanal Janar Waidi Shaibu.
A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaran hedikwatar, Janar Samaila Uba ya fitar, rundunar ta bayyana bidiyon a matsayin ƙagagge da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a gaem da ayyuka da jagorancin sojojin Nijeriya.
A cewar DHQ, bidiyon ba ya wakiltar kowane saƙo a hukumance, wasiƙa, ko muƙamin Babban Hafsan Tsaron ko kuma a shugaban sojojin.
Don haka ne hedikwatar ta kirayi al’umma da su yi watsi da baki ɗaya saƙon bidiyon, tana mai cewa ba daga kowace majiyar sojoji aka samo shi ba.
Binciken sojoji ya nuna cewa akwai alamun jirkita bayanan sadarwar dijital, waɗanda suke nuna ainihin bidiyon ƙirƙirarren fasahar AI ne, don haka kada jama’a su ruɗu da shi.
Haka kuma, hedikwatar ta koka akan abin da ta kira da anfani da fasahar dijital da soshiyal mediya wajen ƙirƙira da yaɗa saƙonnin ƙarya da suka ƙunshi manyan jami’an sojoji.
Akan haka ne rundunar ta yi gargaɗin cewa ire-iren haka ka iya raunana yardar al’umma ga lamuran cibiyoyin tsaro da ƙoƙarin binne ƙoƙarinsu ga tsaron ƙasa, tana mai kira ga gidajen jarida da su, masu sharhi, ‘yan mediya da makamantansu da su ƙaurace wa yaɗa bidiyon saboda faɗa wa haɗari musamman akan tsaron ƙasa.
