Sojoji sun kai samame a maɓoyar ‘yan bindiga, sun kama mutane takwas da ƙwato wasu ababe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na haɗin-gwiwa ƙarƙashin Atisayen FANSAN YAMMA, sun samu nasarori a wasu hare-haren da suka kai kan ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassan jihar Zamfara, inda suka halaka ɗan ta’adda da kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci.

A sanarwar da jami’in yaɗa labarain rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Ɗanja, ya fitar, ya ce sojojin sashe na 2 sun yi artabu da ‘yan ta’adda a ƙauyen Birnin Tsaba da ke ƙaramar hukumar Birnin Magaji a ranar 5 ga Yuni, 2026. Ya ce a yayin musayar wuta, an kashe ɗan ta’adda guda tare da ƙwato babura bakwai.

Sanarwar ta ce, a ranar 6 ga watan Yuni, sojojin sun kai ɗauki bayan wani hari da ‘yan ta’adda suka kai a Anguwar Sarkin Musulmi da ke Kaura Namoda, inda maharan suka tsere zuwa cikin daji bayan arangama da jami’an tsaro.

Haka kuma, bincike ya nuna cewa wasu ‘yan ta’adda sun tare matafiya a hanyar Kaura Namoda zuwa Zurmi tsakanin ƙauyukan Jabanda da Dauran, inda suka kai hari kan motoci biyu.

A yayin haka ne sojoji suka ceto waɗanda suka jikkata tare da kai su asibiti domin samun kulawa akan halin da suke ciki.

A wani samame da aka gudanar a Tudun Wada da Dan Gulbi da ke ƙaramar hukumar Maru, sojoji sun kama mutane takwas da ake zargi da alaƙa da ƴan bindiga, tare da ƙwato babura, na’urorin sadarwa, wayoyin hannu da kayan sarki irin na sojoji.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ta kama wani mutum da ake zargi da karɓar harsasai da aka kama a baya a ƙauyen Tupa da ke Ƙaramar Hukumar Shinkafi.

Kazalika, ta sake jaddada aniyarta ta cigaba da matsa lamba kan ‘yan ta’adda, tana mai kira ga al’umma su riƙa ba hukumomin tsaro sahihan bayanan sirri domin ƙarfafa yaƙi da rashin tsaro a shiyyar da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply