
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An zaɓi Kwamared Hasheem Abdallah a matsayin sabon shugaban Ƙungiyar Malaman Makarantun Polytechnics (ASUP) na Binyamin Usman Polytechnic (BUPOLY) reshen Haɗejia, bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Talata.
A wata sanarwa da aka fitar a yau Laraba, an ruwaito cewa zaɓen, wanda Kodinetan ASUP na Zone A, Kwamared Mohammed Mohammed ya sanya wa ido, Hasheem Abdallah ya samu ƙuri’a 62, wanda ya ba shi damar doke abokiyar karawarsa, Kwamared Nafisa Nasir Ma’aruf, wadda ta samu ƙuri’u 30.
Da yake magana bayan zaɓen, Kwamared Mohammed ya yaba wa mambobin reshen bisa gudanar da zaɓen cikin lumana da ƙoƙarin kiyaye sharuɗɗa da ƙa’idojin dimukraɗiyya.
Ya bayyana zaɓen a matsayin ɗaya daga cikin sahihan zaɓuka da ya taɓa riska a tsawon zangon da ya shafe yana cikin harkokin jagorancin ASUP.
A cewarsa, gudanar da zaɓen bisa tsari ya nuna dattaku, haɗin kai da salon biyayya ga dimukraɗiyya na BUPOLY, yana mai fatan samun shugabanci na ƙwarai ga sababbin jagororin ƙungiyar.
Tuni dai aka rantsar da sababbin zaɓaɓɓun jagororin jim-kaɗan bayan kammala zaɓen ƙarƙashin jagorancin kwamitin zaɓe makarantar, ELCOM.
A nasa jawabin, Kwamared Hasheem ya bayyana godiyarsa ga mambobin ƙungiyar bisa amincewa da shi da kuma tabbatar da zaɓe mai cike da gaskiya da adalci ga kowane ɓangare.
Ya kuma tabbatar musu da cewa zai yi aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki don ganin wa’adin nasa ya yi nasara wajen ciyar da ASUP da BUPOLY gaba.
