Garkuwan Magajin Rafin Sakkwato ya zama wakilin ayyukan Daular Usmaniyya

Spread the love

Daga WAKILINMU, a Sokoto

A cikin wani gagarumin biki da ya haɗa ɗimbin manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya naɗa tsohon Shugaban ƙungiyar Kasuwanci, Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Jihar Sokoto, Alhaji Mu’azu Bello Mai Wurno Garkuwan Magajin Rafin Sokoto, da sarautar Wakilin Ayyukan Daular Usmaniyya, a wani mataki da ya sake jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin masarautun gargajiya da ɓangaren masu zaman kansu wajen ciyar da ƙasa gaba.
An gudanar da bikin ne a Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi da ke Sokoto, inda manyan sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati, fitattun ’yan kasuwa, shugabannin masana’antu, malamai, wakilan al’umma da sauran baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya suka halarta domin shaida wannan gagarumar karramawa.
Da yake jawabi yayin bikin naɗin sarautar, Sarkin Musulmi ya bayyana cewa karrama Alhaji Mu’azu Bello Mai Wurno ba wani abu ba ne face amincewa da irin dogon tarihin hidimtawa al’uuma, riƙon amana, kyautatawa jama’a da kuma gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru wajen bunƙasa tattalin arzikin Jihar Sokoto da ƙasa baki ɗaya.
Mai Alfarma ya ce, sarautun gargajiya ba ado ba ne ko wata alamar ɗaukaka kawai, illa nauyi ne da ke ƙara ɗora wa wanda aka ba su alhakin yi wa al’umma hidima.
“Ba ma naɗa mutane saboda suna ko don ba su matsayi na yin tinƙaho. Muna karrama waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jama’a hidima, tallafa wa al’umma da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa. Alhaji Mu’azu Bello Mai Wurno ya tabbatar da waɗannan kyawawan halaye tsawon shekaru,” inji Sarkin Musulmi.
Sannan ya buƙaci sabon mai sarautar da ya ci gaba da zama wata gada tsakanin masarauta, gwamnati da kuma ɓangaren masu zaman kansu, yana mai jaddada cewa babu yadda za a samu ci gaba mai ɗorewa sai an haɗa hannu tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki.
Ya ƙara da cewa, “Najeriya na buƙatar ’yan ƙasa masu kishin ƙasa da za su yi amfani da dukiyarsu, ƙwarewarsu da tasirinsu wajen amfanar da al’umma. Muna sa ran sabon mai sarautar zai ci gaba da tallafa wa duk wani yunƙuri da zai ƙarfafa zaman lafiya, bunƙasar tattalin arziki da haɗin kan jama’a.”
Da yake mayar da martani bayan karɓar wannan sarautar, Alhaji Mu’azu Bello Mai Wurno ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Majalisar Masarautar Sokoto da Mai Alfarma Sarkin Musulmi bisa ganin cancantarsa da wannan matsayi mai daraja.
Ya ce wannan sarauta ba wai yabo ne kawai gare shi ba, illa wata sabuwar amanar da ke kira zuwa ƙarin hidima ga al’umma.
“Ina miƙa godiyata ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi bisa wannan girmamawa. Ina ɗaukar wannan sarauta a matsayin kira zuwa ga ƙarin ƙaimi na aiki da sadaukarwa. Ina sadaukar da wannan karramawa ga iyalina, abokan hulɗata, al’ummar ’yan kasuwa da kuma duk waɗanda suka mara mini baya a tsawon rayuwata,” inji shi.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da mara wa shirye-shiryen bunƙasa kasuwanci, noma, zuba jari da ƙarfafa matasa baya domin samar da ƙarin damammaki ga al’umma a faɗin Jihar Sokoto da Najeriya baki ɗaya.
A cewarsa, makomar Najeriya tana hannun bunƙasa sana’o’i masu amfani, ilimi, ƙirƙire-ƙirƙire da zaman lafiya tsakanin al’umma, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da tallafa wa duk wani yunƙuri da zai samar wa matasa damar cin gashin kansu tare da inganta rayuwar jama’a.
Mutane da dama daga cikin manyan baƙin da suka halarci bikin sun bayyana cewa wannan karramawa ta zo kan wanda ya dace da ita, suna masu yabawa da irin gudunmawar da Alhaji Mu’azu Bello Mai Wurno ya daɗe yana bayarwa wajen bunƙasa harkokin tattalin arziki, ƙarfafa kasuwanci, tallafa wa harkokin zuba jari da kuma yi wa al’umma hidima.
Har ila yau, mahalarta taron sun bayyana cewa bikin ya sake nuna irin muhimmiyar rawar da cibiyoyin gargajiya ke takawa wajen karrama cancanta, ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa kyawawan ɗabi’un shugabanci, riƙon amana da yi wa jama’a hidima.
Sun kuma yi nuni da cewa, a wannan lokaci da Najeriya ke neman sabbin hanyoyin farfaɗo da tattalin arzikinta tare da ƙarfafa haɗin kan al’umma, haɗin gwiwa tsakanin masarautun gargajiya da ɓangaren masu zaman kansu na ci gaba da kasancewa muhimmin ginshiƙi wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
An rufe taron da addu’o’in neman zaman lafiya, kwanciyar hankali da ɗorewar arziki ga Jihar Sokoto da Najeriya baki ɗaya, yayin da mahalarta suka yaba wa Majalisar Masarautar Sokoto bisa ci gaba da karrama mutanen da ayyukansu da gudunmawarsu ke ƙarfafa tubalan zamantakewa da tattalin arzikin ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply