
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Martaba Sarkin Ilorin kuma Shugaban Majalisar Sarakunan gargajiya na Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya naɗa Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani a matsayin Babban Limanin Masarautar Ilorin.
Kakakin sarkin, Dakta Abdulazeez Arowona ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce, an yi naɗin ne bayan dogon nazari da zaɓe akan al’amarin, inda Imam Fulani ya yi nasarar zama wanda aka zaɓa don riƙe muƙamin daga cikin sauran malaman.
Ya gaji Alhaji Muhammad Bashir Imam OON, wanda ya rasu a ranar 19 ga watan Junairu, 2026.
Sheikh Muhammad Bashir Dasuki mai shekaru 42, jika ne ga babban limani na 8 na Masarautar ta Ilorin, wato Sheikh Ibrahim Dasuki Iman Fulani Agaka kuma ɗa ga limani na 10, Sheikh Maliki bn Dasuki Agaka.
Gabanin naɗa shi a muƙamin, Sheikh Muhammad Bashir shi ne wanda ya kafa Cibiyar nazarin Arabiyya da Musulunci ta Darul Bisharah da ke Airport Egbejila, Ilorin.
Haka kuma, yana ɗaya daga cikin limanan Juma’a na masallacin Afusat Oloriegbe Memorial da ke Oko Olowo a Ilorin.
Bugu da ƙari, mai gabatar da shirin Al-Bisharah Islamic Foundation ne a gidan rediyon Kwara yayin azumin watan Ramadana kuma yana koyarwa a Darul Kitab College of Arabic and Islamic Studies da ke Gaa Akanbi a garin Ilorin.
