Yankunan karkara a Nasarawa sun samu cigaba a mulkin Gwamna Sule – Sani Sidi

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Keffi

Babban darakta na hukumar raya karkara ta Jihar Nasarawa Injiniya Mohammed Sani Sidi yace al’ummomin karkara a faɗin jihar sun samu bunƙasa da cigaba masu ma’ana a cikin shekaru bakwai da Gwamna Abdullahi Sule yayi akan karagar mulki.

Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa ranar Alhamis na mako da ake ciki.

Injiniya Sidi yace cigaban da aka samu na nuni ne da jajircewar gwamnatin jihar wajen inganta rayuwar mutane musamman a matakin karkara.

DG ɗin ya bayyana cewa a cikin shekarun da ake magana a kai gwamnatin jihar ta hanyar hukumar ta aiwatar da manyan ayyuka a yankunan karkaran kamar su gina tituna da magudanan ruwa da makarantu da samar da ruwa mai tsafta da tsaftar muhalli da asibitoci da sauransu.

Yace hukumar na tabbatar daidaitawa da sa baki kan ayyukan more rayuwa, ayyukan zamantakewa da ƙarfafa tattalin arziki da aka mayar da hankali kan yankunan da aka nufa.

Haka kuma yayi amfani da damar wajen bayyana manyan ayyukan hukumar raya karkara inda yace hukumar na da aikin tsarawa da aiwatarwa da kuma sa ido kan shirye-shiryen da aka tsara domin ɗaukaka al’ummomin karkara da kuma rufe giɓin cigaba tsakanin birane da karkara.

Ya ƙara da cewa tun da ya karɓi jagorancin hukumar a cikin shekara guda da ta gabata an samu nasarori da dama ciki har da ɗaukar sabbin ma’aikata da yawa da horar da ma’aikata da aiwatar da ayyukan tituna da dama da kuma sauya ofishin hukumar daga tsohon zuwa sabon wuri da sauran cigaba.

Injiniya Sidi ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yabawa gwamnan jihar Abdullahi Sule bisa nasarorin da aka samu cikin shekaru bakwai na mulkinsa sannan yayi kira ga al’ummar jihar musamman masu zama a karkara da su cigaba da goyon bayan gwamnan domin ya cigaba da aikata kyawawan ayyuka.

Kalmomin Injiniya Sidi sun zo ne dai-dai lokacin da gwamnatin Sule ke cika shekaru bakwai a kan mulki inda raya karkara ke cikin manyan manufofin gwamnatinsa.

Ita dai hukumar raya karkara na aiki ne tare da hukumomin ƙananan hukumomi da abokan hulɗa na cigaba wajen aiwatar da ayyukan da ke da nufin ƙara samun ababen more rayuwa da inganta yawan amfanin gona da samar da dama na tattalin arziki ga al’ummomin karkara.

By ukarofi

Leave a Reply