
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu tashin gobara a wani sashe na ginin Majalisar Dattawa, lamarin da ya haifar da fargaba acikin jama’ar da ke wajen.
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi sa’ar shawo kan wutar cikin gaggawa kafin ta bazu, inda ake zargin ta fara tashi ne daga wani ɗakin girki da ke cikin zauren majalisar.
Hukumomi sun fara bincike domin gano ainihin dalilin tashin gobarar tare da tabbatar da irin ɓarnar da ta yi.
An ruwaito cewa, lokacin da aka yi nasara kashe ta, an yi sa’a ba a sami wanda ya rasa ransa ko jikkata ba, lamarin da ya sa aka koma cigaba da gudanar harkokin cikin lumana.
bayan faruwar al’amarin, ‘yan kwamiti sun umarci ‘yan jarida da su goge hotuna da bidiyoyin da suka ɗauka akan gobarar.
