
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dattawa ta umarci a kama tsohon Shugaban Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari akan ɓatar wasu, maƙudan kuɗaɗe da jimillarsu ta kai Naira tiriliyan 210 da ba a bayyana yadda aka yi amfani da su ba.
Kwamitin majalisar akan Kuɗaɗen Ƙasa ne ya bayar da wannan umarni, bayan binciken da ya yi akan asusun kuɗaɗe da aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin Kyari a lokacin da yake riƙe da muƙamin shugaban NNPC.
Kwamitin ya bayyana cewa akwai gibin bayanai da rashin bayyana amfani da kuɗaɗen, wanda ya sa suka ga dacewar a ɗauki matakin gaggawa na kama Kyari domin ƙara bincike.
Haka kuma, kwamiti ya yi kira ga duk wasu jami’an da ke da hannu ko masaniya kan kudaden da su tabbatar da gaskiya wajen bayar da bayanai.
Wannan mataki da majalisar ta ɗauka ya nuna ƙudirinsu na tabbatar da gaskiya da adalci wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnatin na aikin da aka ɗora masa.
Kazalika, kwamitin, wanda Sanata Ibrahim Ɗankwambo (Gombe ta Arewa) ke jagoranta zai yi amfani da ikon da doka ba shi na bayar da izinin kama Kyari sakamakon zargin sa da ƙin amsa gayyatar majalisar a lokuta da dama.
