
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba ‘yan bindiga suka kutsa makarantar sakandare ta Iluke Bunu a Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu ta Jihar Kogi, inda suka halaka mutum uku ciki har da mataimakin shugaban makaranta tare da yin awon-gaba da wasu ɗalibai a yayin da ake rubuta jarrabawar kammala sakandare (WASSCE).
Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 9:45 kuma an hari ɗalibai masu rubuta jarrabawar ne kai tsaye.
Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun hari makaranta UBE ne a garin, inda ɗalibai daga ƙauyuka uku suek taruwa don rubuta jarrabawar WAEC.
Majiyar ta ce, mataimakin shugaban makarantar Aharha Bunu, MistavGabi Anifowose ya rasa ransa tare da wasu mutane biyu, yakin da aka yi garkuwa da wasu ɗalibai uku da mazauna da dama yayin harin.
Daga bisani Rundunar ‘Yan sandan jihar ta tabbatar da rasuwar mutane uku da suak haɗa da mataimakin shugaban makarantar da wani tsoho, Sunday Jacob Alhassan mai shekaru 70 da kuam wani yaro mai suna Sunday Ayele ɗan shekara shida.
Kakakin ‘yan sandan, ASP Saliu Oyiza ya ce rundunar da ta samu kiran gaggawa tun da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar akan wasu ‘yan bindiga akan kimanin babura 40 sun kai farmaki makarantar da kuma kewayen ƙauyen.
Akan haka ne aka baza jami’an tsaro a yankin domin kwantar hankula al’umma, inda suka yi ba-takashi da ‘yan ta’addan da kora su har zuwa bayan gari.
Haka kuma, rundunar da haɗin-gwiwar wasu hukumomin tsaro ta ƙaddamar da atisayen ceto waɗanda aka sacen da kuma kama dukkan masu hannu aciki.
