‘Yan Nijeriyar da aka kwaso daga Afirka ta Kudu kan ɓangaranci sun isa Legas

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta ce kaso na farko na ’yan Nijeriya da aka kwaso daga Afirka ta Kudu sakamakon hare-haren ɓangaranci da ƙyamar baƙi ya isa Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas da safiyar yau Alhamis.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce ana sa ran jirgin zai sauka da misalin ƙarfe 5:00 na safe.

Sanarwar ta ce jirgin kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace zai tashi daga Filin Jirgin Sama na Oliver Tambo da ke Johannesburg a daren ranar Laraba.

Ebienfa ya ce Gwamnatin Tarayya ce ta ɗauki nauyin gudanar da aikin kwaso mutanen gaba ɗaya, tare da shirya duk wasu matakan tarba da tallafin da za a bai wa waɗanda za su dawo gida.

Ya ƙara da cewa da zarar sun isa Nijeriya, za a yi musu rajista da tantancewa kafin a ba su tallafin da ya dace sannan a haɗa su da iyalansu.

Tun da farko an shirya fara jigilar mutanen ne a ranar Litinin, amma daga baya aka ɗaga zuwa Laraba saboda wasu matsalolin shirye-shirye da suka taso.

By Babaji

Leave a Reply