HOTUNA: Yadda aka yi zagayen gari da kofin da Ivory Coast ta lashe a Gasar AFCON 2023

A ranar Talata mazauna Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast, suka yi dafifi a wasun manyan hanyoyin birnin domin tarbar ‘yan wasan kasar dauke da kofin da suka lashe a Gasar AFCON 2023 da aka kammala a Lahadin da ta gabata.

Ivory Coast ta zama zakaran gasar ce bayan da ta doke Super Eagle na Nijeriya da ci 2 da 1.

Ga karin hotuna daga zagayen garin da aka yi da kofin Abidjan: