Tsaftace zuciya a game da batun kishi (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum. Masu karatu sannun ku da jimirin karanta wannan fili naku na Zamantakewa, wanda ya ke zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Kamar yadda muka fara tattaunawa a makon da ya gabata a game da zafin kishin mata da ya addabi al’umma da abin da yake kawo shi, da kuma yadda za a magance shi, to yanzu za mu ɗora daga inda muka tsaya a makon da ya gabata. A sha karatu lafiya. 

Abu na gaba shi ne, ya ke Uwargida ki sani: kasancewarki ta farko a wajensa ba wayonki ba ne ko dabararki ba ce, ko zaɓinki ba. Allah ne ya ƙadarta cewa ke za ki fara zama matarsa. Kuma ki sani a kan jarrabawa kike. Allah jarraba ki yake don ya ga gudun ruwanki. Kuma ki sani, wannan matsayin naki na Uwargida idan kika yi zalunci zai iya kai ki ga halaka ta Duniya da Lahira. Haka ki sani, shi auren da mijinki ya ƙaro ba wai cin amanarki ya yi ba. Haƙƙinsa ne da Allah Ya ba shi na ya ƙaro mace daga ɗaya zuwa huɗu, idan har zai yi adalci. Saboda haka ɗagawa da ji da kai ba naki ba ne. Da ke da wacce aka auro duk haƙƙinku ɗaya a wajen mijinku.

Haka Allah ya shar’anta. Al’ada ce kawai ta mayar da ke Uwargida. Idan kika yi wasa da haƙƙin Allah kuma kika sa girman kai kika bijirewa Allah, Shi ma zai iya nuna miki mulkinsa a kanki kuma ya zare albarka da walwala a rayuwarki. Shi kansa mijin da kike taƙama, A zare albarkar dake dukiyarsa. Don haka ki daure zuciyarki ki yi komai cikin tsoron Allah. Ke ma ba ki san naki yaran ina za su je ba. Ki sani ita ma Amaryar ba son ranta ne ta aure miki miji ba. Ita ma da so samu ne, za ta samu kamar taki, da ta fi son ta auri mijinta ta zauna daga ita sai shi. Amma ita ma wata jarrabawa ce a kanta da aka ƙadarta ta auri naki mijin. 

Ke kuma Amarya ki sani, ba ƙasƙanci ba ne don Allah ya qadarto miki kasancewa matarsa ta biyu. Wannan yana cikin rubutacciyar ƙaddararki. Ki zauna da amana da kishiyarki da yaranta. Ki sani maza suna ƙara aure ne saboda sun samu ƙarin wadata, ko suna buƙatar ƙaro auren, ko ma wasu dalilan. Ki cire a ranki cewa zai aure ki saboda bai son matarsa ko ta gundure shi. Idan yana da yara ki so su. Wannan shi ne zai nuna kina son ubansu da gaske. Idan ma mutuwa Uwargidan ta yi ko fita ta yi. Ki riƙe mata ‘ya’ya cikin adalci. Sai ke ma Allah ya duba naki. Don ba ki san yadda rayuwa za ta yi da ke ba. 

Amma fa sai kin toshe kunnuwanki. Domin ita Amarya dankali ce sha kushe. Al’ummarmu ta Hausawa kullum ana ganinta a matsayin muguwa ko mai rusa farin ciki wacce ta shiga tsakanin masoya guda biyu. Kuma ba wai a wajen kishiyarta kawai ba. Har ma a wajen sauran matan gari. Ba macen da take yi wa Amarya uzuri sai wacce ‘yarta ko ƙanwarta ko wata ‘yaruwarta za ta yi aure ko ta yi aure  ta je a matsayin ta biyu. Kuma ƙaddara ce da za ta iya faruwa kan kowacce mace.

  Amarya ki sani, idan kika samu fada a wajen miji kada ki zalunci kishiyarki ko yaranta. Ke ma idan Allah ya ba ki ‘ya mace ba za ki so kishiya ta azabtar da ita ko yaranta yadda kika azabtar da wata ko ‘ya’yanta ba. Haka ku dinga kula da haƙƙin dangin miji, musamman mahaifi da mahaifiyarsa. Domin watarana ku ma iyayen miji ne. Ba za ku so a gallaza muku yadda kuka gallaza wa surukanku ba. 

Haka zalika, akwai kuma dangin miji da suke ƙoƙarin dole sai sun kawo ruɗu da rashin zaman lafiya a cikin gidan ɗan’uwansu. In dai ɗanuwansu ya zauna lafiya da matarsa, to sai a shiga zargin ta magance shi ne. Ba biyayyarta ko halayen kirkinta ya sa yake sonta ba. Babban abin takaicin shi ne, ƙannen miji musamman ma mata su ne suke fara assasa matsalar.

Uwar miji in dai dattijuwar arziki ce mai addini ba za ta bi wannan yariman ta sha kiɗa ba. Amma abin takaici, ita ma sai ta zama ‘yar amshin shatan ‘ya’yanta. Haka idan mijin na da ƙanne ko yayye maza, idan masu biye mata ne, nan ma a sake samun masu bin ayarin muzguna wa matar yayansu. Wani lokacin ma har da kishin sauri.

Wato kishin da ake yi tsakanin matar wa da ƙani (faccaloli). Shi kuma wannan ma ya fi kowanne muni. Don zai iya sanadiyyar da za ta sa ‘yanuwan jini su zama abokanen gabar juna. Saboda kawai matansu ba sa jituwa. Kuma kowa yana goyon bayan tasa.  Waɗannan misalai suna da yawa idan na ce zan ta  lissafowa, filin nan ma ba zai isa a gama lissafo su ba. 

Kada mai karatu ya manta fa duk waɗannan halaye da na lissafo a sama, mata sukan tsinci kansu suna aikata su ne kawai idan namiji ya gifta a cikin alaƙarsu da mace ‘yaruwarta. Kuma kishi shi yake haddasa hakan. Kowacce daga cikin matan tana neman samun matsayi ma fi girma daga wajen namijin. Kuma tana ganin haqanta ba zai cim ma ruwa ba har sai ta dusashe tauraruwar wata.

‘Ki faɗa wa Shugaban Ƙasa akwai yunwa a ƙasa’ – Cewar Sarkin Kano ga Uwargidan Shugaban Ƙasa

Tsaftace zuciya a game da batun kishi (1)

Wanda hakan son zuciya ne mai girma. Haka a musulunce, a al’adance ko a mu’amalance bai dace ba. Daga ƙarshe ina kira ga ‘yanuwa mata da su zama masu tausayawa da adalci ga ‘yanuwansu na jinsi. Ki sani, idan kika zama sanadiyyar ƙuntata wa rayuwar wani ko wata, to ke ma ko ba daɗe, ko ba jima; za ki girbi abinda kika shuka.

Zan dakata a nan. Ina jinjina ga masu kira su ba da shawara ko tsokaci. Haƙiƙa kuna raina har kullum kuna ƙarfafata. Na gode.