Amarya ta yi wa angonta yankan rago a Neja

Daga BASHIR ISAH

Ana zargin wata amarya mai suna Aisha Aliyu a kauyen Nasarawa cikin Karamar Hukumar Lapai a Jihar Neja, da kashe mijinta Idris Ahmadu ta hanyar yi masa yankan rako.

Majiyarmu ta ce Aisha ta yi ajalin angon nata ne makonni shida da yin aurensu.

News Point Nigeriya ta rawaito cewar, lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 1:00 na tsakar dare.

Bayanai sun nuna an samu rashin jituwa a tsakanin ma’auratan da yammacin Lahadin da ta gabata, inda aka shiga tsakani aka sulhunta su. Amma bayan da dare ya tsala sai mahaifiyar marigayin ta jiwo ihun danta.

“Ko da mahaifiyar tare da sauran mazauna gidan suka fito, sai suka tarar da marigayin kwance cikin jini male-male. Ya yi yunkurin ficewa daga dakin amma ya zube a bakin kofa. Kuma har yanzu ba a san inda matar take ba,” in ji majiya.

Majiyar ta kara da cewa, da farko sai da ta daba wa marigayin wuka a kirji, kafin daga bisani ta yi masa yankan rago.

An ce kafin auren nasu ma’auratan sun yi soyayya na shekaru da dama, amma kafin saka ranar aure sai yarinya ta sauya ra’ayi kan cewa wani daban take so ta aura. Wanda daga bisani aka shawo kanta, ta kuma amince aka daura auren.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar lamarin, tare da cewa suna zurfafa bincike.