Daga BASHIR ISAH
Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya karrama ‘yan wasan Super Eagles da lambar yabo ta MON hadi da tukwicin fili da gida a birnin tarayya Abuja.
Tinubu ya yi wa ‘yan wasan goma ta arzikin ne a ranar Talata a lokacin da ya karbi bakuncinsu tare da jami’an Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya (NFF) a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Tawagar ta ziyarci Tinubu ne bisa jagorancin Ministan Bunkasa Wasannin Motsa Jiki, Saenata John Owan Enoh.
Wata sanarwar da ya fitar, Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, ya ce Shugaba Tinubu ya yaba wa tawagar Super Eagles bisa bajintar da suka nuna da kuma nasrar da suka samu a gasar.
