‘Yan Arewa sama da 20,000 sun samu aikin a MTN sanadiyyar Amina Magaji Danbatta – Dr. Sarari

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar abokan mu’amala da kamfanin MTN a Arewa, wato Customer Acquisition Partners CAP, sun gudanar da taron karramawa ga Hajiya Amina Usman Danbatta wacce ta riƙe Babbar Manajan Kamfanin MTN a yankin arewacin Nijeriya.

Taron ya gudana ne a ranar Asabar da ta gabata a Bristol Hotel da ke cikin birnin Kano.

Kafin yajiye aikinta a ranar 31 ga Oktoban 2023, Hajiya Amina ta shafe shekara 21 tana aiki da Kamfanin MTN a matsayin manaja a shiyyar Arewa.

Dr. Ahmad Muhammad Sarari shi ne shugaban Kamfanin Sarari Clasiq, ya bayyana cewa dauba irin gudunmwar da Hajiya Amina ta bayar wajen samar wa ‘yan Arewa aiki ya sa suka shirya taron musamman don karrama ta.

Ya ce, “Hajiya Amina ta samar wa mutane sama da 20,000 aiki.

“Lallai ta gaji mahaifinta Magaji Danbatta wajen haƙuri da jajircewa da riƙon amana, ita abin koyi ce ga al’ummar ƙasar nan.”

A nata jawabin, Hajiya Amina ta yi godiya ga CAP bisa wannan taro da suka shirya mata.

Ta ce “jajircewa da aki tuƙuru ne suka kai ni ga wannan matsayi, don haka nake kira ga al’umma da su ba da himma kuma a yi aiki tukuru kana a yi haƙuri, to nasara tana zuwa.”

Taron wanda membobin CAP na jahohin Arewa suka shirya, ya samu halartar manyan jami’an Kamfanin MTN a shiyyar Arewa da sauran baƙi daga sassa daban-daban.

By Editor