Zaɓen cike gurbi: Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa ya rantsar da mambobi biyu

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Honorabul Danladi Jatau, ya rantsar da mambobin majalisar biyu wadanda suka lashe zaben cike gurbi wanda aka gudanar a karshen mako da ya gabata a mazabunsu.

Mambobin biyu da aka rantsar su ne; Hon. Mohammed Adamu Omadefu (APC Keana) da Hon. Musa Ibrahim Abubakar (NNPP Doma ta Kudu).

A jawabinsa a lokacin da yake rantsar da sabbin ‘yan majlisar a zauren majalisar da Lafiya Fadar Gwamnatin jihar, Kakakin Majalisar, Danladi Jatau, bayan ya taya ‘yan majalisar murna dangane da sake mallakar kujerunsu a majalisar, ya kuma kalubalence su da su ci gaba da gudanar da wakilci nagari wa al’ummarsu a koyaushe.

Ya ce, “Da farko ina so in taya ku murna dangane da nasarar da kuka samu a zaben cike gurbi da aka gudanar kwanan nan. Muna murnar sake mallakar kujerunku a wannan majalisar,”  in ji shi.

Daga nan Hon. Jatau ya bukace su da su tabbatar sun cika rantsuwa da suka dauka inda ya kuma  yi kira ga al’ummomin mazabunsu su ci gaba da ba su cikken goyon baya don ba su damar samun nasara.

A nasu bangaren, da suke maida martanin jawabi wadanda rantsarwar ta shafa, sun gode Allah da kuma al’ummomin mazabunsu da suka sake fitowa kwansu da kwarkwata suka sake mayar da su majalisar ta hanyar ba su kuri’un su.

Zargin lalata abu ne da ke faruwa a kowacce masana’antar fim – Maje El-Hajeej 

‘Yan Arewa sama da 20,000 sun samu aikin a MTN sanadiyyar Amina Magaji Danbatta – Dr. Sarari

Sun kuma gode wa Shugaban Majalisar Dokokin dangane da shugabanci nagari da yake yi a majalisar inda suka tabbatar masa cewa za su ci gaba da hada kai da shi don a sira tare.

Idan za a iya tunawa, a ranar 28 na watan Nuwamban shekarar 2023 ne wata Kotun Daukaka Kara da ke zama a Abuja ta bayyana zabukan mazabun biyu a jihar, wato Keana da Doma ta Kudu a matsayin wadanda ba a kammala ba inda ta umurci a sake gudanar da sabon zabe.