Zargin lalata abu ne da ke faruwa a kowacce masana’antar fim – Maje El-Hajeej 

“Ni ne marubucin da ya fara siyar da labari mafi tsada a Kannywood”

Daga AISHA ASAS 

Masana’antar Kannywood cike take da haziƙan marubuta da aka jima ana shan romon baiwar da suke da ita, duk da cewa a harkar fim suna ɗaya daga jerin mutanen ɓoye, sai dai hakan ba yana nufin muhimmancinsu ga fim kaɗan ne ba, domin marubuci shine zuciyar kowane fim. 

A wannan makon, shafin Nishaɗi ya ɗauko wa masu karatu ɗaya cikin manyan marubutan da masana’antar Kannywood ke alfahari da su, hakazalika mai shirya finafinai da ya samar da finafinai na ji da faɗa a Ƙasar Hausa. 

Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Maje El-Hajeej Hotoro:

MANHAJA: Sunanka sananne ne, don haka tarihin rayuwarki ne abin buƙatar masu karatunmu.

EL-HAJEEJ: Sunana Maje El-Hajeej Hotoro. An haife ni a unguwar Hotoro da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano a shekarar 1978. 

Na yi karatun firamare a Hotoro South Primary School daga nan na wuce Government Secondary Yargaya shekara uku, sannan na ƙarasa a Rumfa College. Na kuma samu diploma a Legal. Na yi diploma a harkar komfuta sannan na yi kwas na musamman a fannin Turanci a Landan. Ina da mata da ya’ya biyu, Muhammad da Khadijah.

Na yi tafiye-tafiye da dama a gida Najeriya da wasu ƙasashen ƙetare. Ni marubucin litattafai da finafinan Hausa ne, ɗan jarida, mawallafi, manazarci kuma mai shirya finafinai da shirye-shirye na musamman ga gidajen talabijin da kafofin sadarwa na zamani.

Ko za ka iya sanar da mu dalilin da ya sa ka zaɓi ɓangaren shirya finafinai?

Da farko na fara ne da rubuta labarin fim mai suna ‘Malika’ wanda Aminu Saira ya bayar da umarni ya kuma samuwa karɓuwa sosai. Sai na ci gaba da rubuta wa irin su ‘Shu’uma’, ‘Matan Gida’, ‘Zawarawa’ da sauransu, daga baya sai na ga akwai buƙatar na faɗaɗa tunanina ta hanyar mallakar kamfanin shirya finafinai mai suna Sirrinsu MEDIA, sai na fara da shirya shirye-shirye na bincike da rahotanni, daga baya sai na fara shirya finafinan barkwanci, daga baya na koma finafinai masu dogon zango da ‘Macen Sirri’.

Na kuma zaɓi shiryawa ne saboda ba wa ƙananan jarumai maza da mata dama da suka rasa dama a wasu wurare, na kuma yi nasarar sanya su a finafinana da yawan su ya haura 200.

Wacce shekara ka shigo masana’antar fim?

Na shigo Kannywood tun 2000.

Ko za ka iya tuna fim na farko da ka shirya?

Fim na farko shi ne ‘Juyayi’. Na kuma fuskanci babban ƙalubale saboda rashin sanin makamar aiki da rashin gogewa.

Ko kwalliya ta biya kuɗi sabulu a lokacin da fim ɗin ya kai ga masu kallo?

Gaskiya a lokacin kwalliya ba ta biya kuɗin ruwa ba ma ballantana na sabulu. Domin an shiga rikici da kuma asarar dukiya.

Bari mu koma ɓangaren finafinan da ka rubuta. Adadin su zai kai nawa zuwa yanzu?

‘Malika’, ‘Shu’uma’, ‘Matan Gida’, ‘Zawarawa’, ‘Kowa Darling’, ‘Uwar Gulma’, ‘Hangen Dala’, ‘Macen Sirri’, ‘Gidan Duniya’, ‘Sirrin Boye’, ‘Wacece’, ‘Karima’, ‘Ki je kya gani’, ‘Mai Dalilin Aure’, ‘Kauyawa’, ‘Siyasa’, ‘Nuratu’, ‘Wacece Sarauniya’, ‘Yar Mai Ganye’.

Me za ka ce game da zargin da ake yi wa wasu masu shirya fim na lalata da mata kafin su ba su damar fitowa finafinansu?

Zargin lalata da mata abu ne da ya ke faruwa a kowacce masana’antar shirya finafinai na duniya, Hollywood, Bollywood, Nollywood da kuma Kannywood. Abinda na sani ƙarfe ɗaya baya amo, idan an nemi lalata da yarinya ta ce ba zata yi ba mana, fim hanyar shiga aljanna ce? 

A kowane ɓangarori na rayuwa ana samun nagari da na banza, malaman jami’a ana zargin su da lalata da ɗalibai don su ba su maki, ana zargin ma’aikatun gwamnati da dama da lalata da mata don a ba su aiki, don haka a Kannywood idan an samu wasu na aikata hakan ba wani abin mamaki ba ne.

Amma dai koma mene ne ba zai yiwu ace kowa haka ya ke ba. Sannan sai bango ya tsage ƙadangare ya ke samun wajen shiga, idan mace ta kame kanta ba wanda ya isa ya yi lalata da ita dole.

Idan ta je wani waje aka faɗa mata haka sai ta tafi wani wajen, idan ba dama ta haqura. Sannan da yawa matan ba sa biyo hanyar da ya dace a sa su a fim sai su bi duk wanda suka ga ya yi hoto a ‘location’ ko da wani ɗan fim ba tare da sanin wanene shi ba.

Baya ga haka da yawa alhakin iyayensu ne yake kama su domin sun gudu sun bar gida ba sanin iyayensu, wasu zawarawa ne sun ci amanar mazan su da ya’yansu sai su haɗu da ‘yan shan kai su yi abinda suka ga dama da su.

A ‘yan kwanakin baya ne masana’antar finafinai ta Arewa ta yi nasarar shigar da fim ɗinta a ‘Netflix’ karo na farko, wanda hakan ya sa wasu ke tambayar me ya sa ba a yi ba sai bana. Ko za ka iya sanar da mu yadda lamarin yake?

Dalilin shine a baya ba mu da gogewar fasahar sadarwa na zamani da kayan aiki da kuma hanyoyin samun kuɗaɗen da za a zuba a yi fim ɗin da zai kai matsayin da za a kai shi manhajar Netflix.

Wasu na ɗora alhakin rashin yawaitar finafinan Hausa a Netflix kan rashin ingancin su. Ko akwai gaskiya a zancen?

Gaskiya ne akwai rashin inganci da kuma wadataccen ilimin kimiyya da fasaha na sarrafa kayan aikin zamani da kuma rashin jami’an da za su yi mana jagoranci su haɗa alaƙa da masu manhajar.

Wanda a halin yanzu sun yi tattaki sun zo an zauna da su an kuma fara shirye-shiryen yin irin finafinan da za su dace da muradun su.

A naka tsari idan yarinya ta zo da sha’awar zama jaruma, waɗanne sharuɗɗa ne za ta cika kafin ka amince da sanya ta fim?

Amincewar iyaye, rajistar kamfani mai ɗauke da dokoki da kuma ƙa’idoji, rajistar hukumar tace finafinai da kuma rajistar ƙungiyar ‘yan fim, sannan na ba ta shawarwari.

Idan mun koma ɓangaren masu rubutu finafinai, da yawa daga ciki babban ƙorafin da suke yi shi ne rashin biyan su haƙƙinsu idan sun yi rubutu. A matsayinka na marubucin fim kafin ka zama mai shiryawa ko a naka ɓangaren ka fuskanci wannan ƙalubale?

Gaskiya ban taɓa ba.

Marubuci shi ne zuciyar kowanne fim, sai dai har zuwa yanzu marubuta finafinai ba su gamsu da irin matsayin da ake ba su a masana’antar fim ba. Me za ka iya cewa kan wannan?

Shakka babu marubuci shine zuciyar kowane fim, amma da yawa masu shirya wa ko masu bayar da umarni sun fi daraja jarumai akan marubuci. Shi marubuci yana cikin mutanen ɓoye, waɗanda ayyukan su aka sani ba su ba. Don haka wasu ke ganin ba wani gudunmawa suke bayar wa a harkar fim ba.

Ta ya ka ke ganin za a iya ƙara inganta finafinan Hausa har su dinga gogayya da na ƙasashen ƙetare?

Nagartaccen labari da ya samu ingantaccen rubutu mai cike da bincike. A yi amfani da ilimi wajen gudanar da aikin, sannan a ɗauko gogaggun ma’aikata da jarumai.

Za mu so sanin ƙalubalen da ka ci karo da su tun daga shigowar ka masana’antar fim kawowa yanzu.

Haɗuwa da mutanen da ba su da ilimi masu cike da wauta, asarar dukiya a wasu lokutan, rashin wadataccen lokaci na gudanar da rayuwa ta. Mutanen da suka zo gare ka don neman taimako amma a ƙarshe su koma suna yaɗa sharri a kanka.

Ko za mu iya sanin wasu daga nasarorin da ka samu?

Na zama marubuci na farko da ya fara sayar da labari mafi tsada a Kannywood (Sirrinsu) wanda a 2000 aka saye shi N100, 000. Na samu kyautar gwarzon marubuci, na haɗu da mutane masu daraja da suka yi min rana a rayuwa. Na horar da matasa maza da mata da dama. Na ba wa marasa dama sun kuma yi amfani da damar sun zama wasu. Na samu alaƙa da kafar dillancin labarai da finafinai na ƙasar waje da suke ba ni aiki.

Wacce shawara za ka ba wa sababbin marubutan fim?

Su dage da bincike akan sabbin abubuwa su kuma faɗaɗa bincike da tunani, sannan su riƙa kallon manyan finafinai na ƙetare don samun ƙarin basira.

Wane kira za ka yi ga mata da suke ciki da kuma masu sha’awar shiga harkar fim?

Su sani ita shahara tana da farashi dole kuma sai an biya. Ma’ana su fitattun mutane ba su da sirri, dole su riƙa tattalin mutunci da ƙimar su, domin samun shaida mai kyau a wajen yan kallo. Duk wacce za ta shiga fim ta nemi shawarar iyayenta idan ba sa so ta haƙura. Sannan ta tabbatar ta yi bincike akan wajen wanda za ta je, idan ya zo mata da maganar banza ta haƙura, ta ƙara gwada wani wajen.

Idan ta samu shiga ta zama jakadiya tagari, kada ta zubar da mutuncinta da kuma kunyata iyayenta.

Mun gode.

Ni ma na gode.