Wane ne Dr. Aliyu Ishaq Namangi?

Daga MOHAMMED BALA GARBA

Aliyu Namangi Malami ne, kuma mawaƙi mai wa’azi, wanda ya fito daga wani ƙauye mai suna Mangi a kusa da ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduna, a Arewacin Nijeriya. Wakoƙinsa sun yi matuƙar tasiri wajen ilmantarwa da karantarwa game da sukar mulkin kama-karya. Sufi ne mabiyin tafarkin Sufaye. 

Masana da manazarta da dama sun kawo tarihin Aliyu Namangi a aikace-aikacensu da suka gudanar, ire-iren waɗannan ayyuka na manazarta kan Aliyu Namangi sun haɗa da Skinner (1969) da Ɗangambo (1973) da Hassan (1973) da Birniwa (1989) da Yakawada (1987) da Sankalawa (2005) da Muhammad (2010) da Muhammad (2011) da Nazifi (2011).

Dukkansu sun bayyana cewa an haifi Aliyu ne a wani ƙauye mai suna Mangi a kusa da birnin Zariya. Hijira na da shekara dubu ɗaya da ɗari uku da goma sha biyar (1315) A.H. wacce ta yi daidai da shekara ta dubu ɗaya da ɗari takwas da casa’in da huɗu (1894) A.D. A ranar Larabgana wato Larabar ƙarshen watan Safar, wato watan biyu na Musulunci.

An kuma haife shi ne a lokacin sarkin Zazzau Kwasau, sunan mahaifinsa Ishaq, sunan mahaifiyarsa kuwa Hauwa’u. An haifi Aliyu Namangi lafiyarsa ƙalau kamar sauran jarirai. Bayan shekara ɗaya da haihuwarsa a watan Safar sai idanunsa suka tsiyaye a sakamakon rubdugun cutar ‘ƙyanda’ da ta ‘Agana’ da suka same shi a lokaci ɗaya. Wannan shi ne musabbabin makancewar Aliyu Namangi, kuma an yi masa kaciya yana da shekara bakwai da haihuwa. (Yakawada, 1987:6-8).

An taɓa ba ni labarinsa da cewa, watarana wani Sarki ya shirya taron Makafi amma sai Aliyu Namangi ya ƙi zuwa. Sai Sarkin ya aika aka kirasa. Da ya zo sai ya tambaye shi me ya sa ya shirya taron Makafi amma bai zo ba?

Sai ya cewa Sarki ni ba Makaho ba ne, domin ina da wani haske a zuciyarta wanda nake gani da shi. Da ni Makaho ne da ba zan ga layun da aka binne a ƙarƙashin kujerarka ana son a kashe ka ba. Sarki ya yi farat ya sauƙa daga kan kujerar, fadawa suka tona wajen sai ga layu a binne.

Dr. Aliyu Namangi ya tava yin ru’uya da mahaifiyar Annabi (Sallalahu alaihi wasalam), wato Nana Aminatu ‘yar Wahbi, inda ya bayyana hakan ƙarara a babin na uku cikin waƙarsa ta yabon Annabi (Sallalahu alaihi wasalam) da cewa:
Albishirinku masoya Allah,
Na ga Amina cikin barci na.

Wadda ta haifi Rasulullahi,
Watan Ramalana a barcin rana.

Na nemi ta sami zama mu yi taɗi,
In cusa shi a waƙoƙi na.

Ban samu ba sabo da larura,
Don shi na koki rashin halina.

Nai fata tahowar fa dalilin,
In koma Makka ne wata rana.

Ko ya zamo shi ne sanadiyyar,
In ga Rasulu cikin barci na.

Barkan mu da wannan lokacin.