‘Ku mara mini baya don kwalliya ta biya kuɗin sabulu’ – Baffa Bello

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a kno

An buƙaci al’umar yankin Ƙaramar hukumar Minjibir da ke Jihar Kano da su bai wa Sabon kantoman riƙo na yankin ta yadda zai sami damar aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa don amfanin jama’ar yankin.

Sabon kantoman riƙo na yankin Minjibir, injiniya Baffa Bello, shi ne ya buƙaci hakan a ranar Litinin jim kaɗan da karɓar ragamar aiki daga hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar mai barin gado, Hon. Sale Ado Minjibir.

Kafin tabbatar Baffa Ado a matsayin sabon kantoman riƙon na shiyyar ta Minjibir, ya kasance Darkta na sashen kula da ma’aikata na hukumar yankin.

‘Ki faɗa wa Shugaban Ƙasa akwai yunwa a ƙasa’ – Cewar Sarkin Kano ga Uwargidan Shugaban Ƙasa

Gobara ta kama ofishin ‘yan sanda a Kano

Baffa Bello, ya yi amfanin da wannan dama wajen yaba wa gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf kan yadda take ƙoƙari wajen ɗabbaƙa ayyukan more rayuwa don amfanin al’umar Kano.

Inda ya yi fatan da yardar Allah kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, musamman idan ya samu goyon bayan jama’ar yankin