Daga BASHIR ISAH
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta ce babban ofishinta na shiyya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Nasarawa a jihar ya kama da wuta.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Mr Hussaini Gumel ne ya tabbatar da afkuwar hakan ga Kamfanin Dillanci Labarai na Nijeriya (NAN) a Kano, inda ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin.
A cewarsa, ‘’Gobara ta kama a hedikwatar ofishin shiyya da misalin ƙarfe 5:45 na asuba inda sashe mai yawa na ginin ya ƙone ƙurmus.
‘’Hakan ya faru ne duk kuwa da ƙoƙarin Hukumar Kashe Gobara ta yi wajen kashe wutar,” in jami’in.
Ya ci gaba da cewa, tuni an fara gudanar da binciki domin gano sasabin gobar.
Jami’ar Aliko Ɗangote ta dakatar da malamin da ya sa ɗalibai gwale-gwale
Ya ce ‘’An kewaye wurin da gobarar ta auku domin hana ɓata-gari shiga su wawushe kaya, kuma babu abin da ya sami bindigogi da alburusai da ke ofishin.
‘’Shugaban ‘yan sandan yankin na ci gaba da tantance abubuwan da gobarar ta shafa.”
