Jami’ar Aliko Ɗangote ta dakatar da malamin da ya sa ɗalibai gwale-gwale

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil a Jihar Kano ta dakatar da wani malami bisa sanya wasu ɗalibai tsallen-kwaɗo da ɗaga hannu a aji.

Daily Nigerian ta rawaito cewa wani faifan bidiyo ya nuna yadda wani malami ya saka wasu ɗalibai tsallen-kwaɗo ana tsaka da darasi a aji.

Bidiyon ya haifar da cecekuce da kuma alla-wadai da ga mabiya shafukan sadarwa.

Sai dai hukumar jami’ar, a wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Sa’idu Nayaya ta ce tuni jami’ar ta ɗauki matakin dakatar da wannan malami.

Jami’ar ta ƙara da cewa tuni an fara gudanar da bincike da nufin ɗaukar matakin da ya dace.

“Hukumar jami’ar ta na tabbatar wa iyaye cewa za ta ci gaba da kare lafiyar ‘ya’yansu.

“Jami’ar ta kuma jaddada ƙudirin ta na samar da yanayin karatu mai kyau ga ɗalibai,” in ji wani ɓangare na sanarwar.

By Editor