Tsaro: Hukumomin Abuja sun bai wa masu zama ƙasan gada wa’adin tashi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar kula da birnin Abuja ta bai wa ɗaruruwan mutane da ke zama a ƙarƙashin gadojin da ke birnin mako guda su tashi ko kuma su fuskanci fushin hukumar.

Mai taimaka wa ministan birnin na Abuja kan muhalli da kawar da shara, Fred Kpakol ya ce sun ɗauki matakin ne sakamakon koken da mazauna birnin ke yi kan ƙwace da fashi da ake yi wa al’umma.

Fred Kpakol ya ce gadojin da ake fuskantar wannan mastaala da aka umarci waɗanda ke zaune a kasansu sun haɗa da gadojin unguwannin Garki, Wuse II, Maitama, da Wuse.

Haka kuma ya yi gargaɗin cewar waɗanda ke zaune a ƙarƙashin irin waɗannan gadoji a ciki da wajen Abujar da su gaggauta barin wuraren saboda nan ba da jimawa ba za a ƙaddamar da wata runduna ta ‘Operation Storm under the bridge’, don ganin sun kakkaɓe birnin daga bazanarar tsaro da ake fuskanta.

By Editor