Hauhawar Farashi: Dole gwamnoni su sauke nauyin da ke kansu – Fasua

Daga WAKILINMU

An nuna buƙatar da ke gwamnonin jahohin ƙasar su duba tare da sauke nauyin al’umma da ya ɗauru a kansu domin samun daidaiton rayuwa

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan sha’anin tattalin arziki, Mr Tope Fasua ne ya yi wannan kira.

A cewarsa, ya zama wajibi gwamnonin jihohi su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar amfani da kuɗaɗen da gwamati ke ba su wajen biyan basussukan albashi, fansho, haƙƙoƙin ‘yan kwangila da tallafi.

Tope ya ci gaba da cewa, “A ƙarshen makon nan na yi bincike a kasuwanni kan hauhawar farashin ababen masarufi, abin babu daɗin ji, na kuma sanar da shugabanni.

“Amma kada mu manta Gwamnatin Tarayya ta ninka abinda take bai wa jihohi na kuɗaɗen gudanarwa tun bayan cire tallafin mai amma babu wani canji na a zo-a-gani daga ɓangaren jihohin kuma wannan kuskure ne.

“Don Allah su biya basussukan albashi, garatuti da fansho; su biya ’yan kwangilar da ke bin su bashi; su bayar da sabbin kwangiloli cikin gaggawa don yin manyan ayyukan da ka iya taɓa rayuwar al’ummarmu. Misali, manyan hanyoyi da gidaje.

“Mutanenmu na buƙatar ɗauki na gaugawa daga baraznar tashin gwauron zabi na tsadar rayuwa.

“Haba! Wake robar fenti Naira 5,000; manyan doya guda biyar sun doshi N9,000; kwandon albasa Naira 3,000, na ji ba daɗi, amma yaya za a yi? Su ma ‘yan kasuwar ƙoƙarin ceton kansu suke.

“Bai kamata a ce hukumar ƙididdiga ta Ƙasa ta riƙa kawo mana sabbin ƙididdigar hauhawar farashin kayayyaki a kowane wata muna kwance muna barci muna jiran wata mai zuwa ma mu ji wani sabon labarin ba.

“Hanya mafi ɓullewa da nake hangowa ita ce, a samar da hanyoyin wayar da kan jama’a, kan matakan rigakafi kan hauhawar farashin kafin aukuwarsa da na daƙile shi idan ya zo.

“Yanzu ne lokacin da ya fi dacewa da ɗaukar wannan tsarin wato lokacin da hauhawar farashin kaya ta kai kashi 28.92 cikin 100 a cikin shekaru 24.

“Ba kawai kukan hauhawar farashin ko ɗaukar matakai bayan faruwarsa ne abin da Nijeriya ke buƙata ba.

“Daga yanzu har nan gaba, muna buƙatar aiwatar da wasu tsare-tsare da manufofin da za su taimaka mana wajen magance hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar da ba za a sake fuskantar hakan ba a nan gaba,” in ji Tope.