Ministocin ECOWAS sun gana a kan batun Burkina Faso, Mali da Nijar

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen Mambobin Ƙungiyar ECOWAS sun gana a ranar Alhamis a Abuja, karon farko bayan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar, yayin da a vangare guda kuma shugaban aasar Senegal, Macky Sall ya dage babban zaɓen ƙasar.

Taron Ministocin ya zama sharar-fage ga taron da shugabannin ƙasashen ƙungiyar za su yi don tunkurar waɗannan matsalolin.

Gwamnatin Zamfara ta fara biyan tsoffin ma’aikatanta bashin giraduti na N13.4bn

Taron, kamar yadda wata sanarwar da ƙungiyar ECOWAS din ta wallafa a shafinta na intanet ta nuna, taro ne na musamman da ya ƙunshi ‘yan kwamitin shiga-tsakani da majalisar tsaro a matakin ministoci, wanda sanarwar ta ce za su yi zama da nufin tattaunawa a kan halin da yankin Afirka ta yamma ya samu kansa a ciki ta fuskar tsaro da wasu matsaloli da suka jibanci siyasa.

Tun a ranar 28 ga Janairu ƙasashen Mali da Burkina Faso da Kuma Nijar suka sanar da aniyar ficewa ƙungiyar ECOWAS.

By Editor