Daga MAHDI M. MUHAMMAD
An kashe mutane uku ciki har da wani sifeton ‘yan sanda a ranar Laraba a wani sabon harin da ’yan Boko Haram suka kai a garin Kukareta da ke ƙaramar hukumar Kaga a jihar Borno.
An tattaro cewa ’yan ta’addan sun ƙona jami’in ɗan sandan tare da wani gini.
Sun kuma kwashe makamai da alburusai a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
An harbe wasu fararen hula biyu tare da ƙona motar hakimin gundumar tare da motar ƙirar Hilux guda ɗaya na rundunar haɗin gwiwa ta farar hula da ke aiki a wannan yankin.
Tsaro: Hukumomin Abuja sun bai wa masu zama ƙasan gada wa’adin tashi
Kira ga gwamnati kan ƙalubalen tsaro a Nijeriya
A cewar wata majiya daga cikin jami’an tsaron, motar kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta arewa maso gabas, Operation Hadin Kai, a ziyarar da ta kai wurin da lamarin ya faru, ta taka wata na’urar fashewar bama-bamai (IED) wadda ta tarwatsa motar kwamandan tare da raunata direban a ƙafarsa yayin da kwamandan da wani ma’aikaci ba su ji rauni ba.
Harin na baya-bayan nan na zuwa ne kwanaki biyar bayan wani harin makamancin haka ya yi sanadin mutuwar jami’an ’yan sanda huɗu a Gajiram, hedkwatar ƙaramar hukumar Nganzai.
