Kira ga gwamnati kan ƙalubalen tsaro a Nijeriya

Spread the love

Nijeriya dai wata babbar ƙasa ce a yammacin Afrika, wacce Allah ya albarkace ta da tarin ni’imomi da albarkatu masu yawa. Kama daga yawan jama’a da suka haura miliyan 200, da kuma ma’adinan ƙarƙashin ƙasa, na ruwa da na kan tudu, wanda ba kowacce ƙasa ce Allah ya bai wa wannan arzikin ba. Sai dai kuma ƙalubale iri iri da suka haɗa da rashin shugabanci nagari, cin hanci da rashawa, ƙabilanci da ɓangaranci, da kuma uwa uba matsalar tavarvarewar tsaro.

Sai dai duk da ƙoƙarin da masu riƙe da madafun iko, ƙwararru da rundunonin tsaron ƙasa suke cewa suna yi don shawo kan waɗannan matsaloli da suka dabaibaye ƙasar nan, har yanzu haƙa ba ta cimma ruwa ba.

’Yan Nijeriya na ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da talauci, harkokin tafiyar da gwamnati sai ƙara lalacewa suke yi saboda rashin kishin ƙasa da ayyukan rashin gaskiya da suka yi yawa, ga kuma ƙaruwar ƙungiyoyin ’yan ta’adda da tsagera da suka yi yawa a cikin ƙasa, suna haifar da firgici a zukatan ’yan Nijeriya da asarar rayuka da dukiyoyi.

Lallai akwai buƙatar hukumomi su tashi tsaye su ga sun samar da sauyin dabaru da tsari a irin matakan da suke ɗauka, saboda rayuwa kullum ƙara sauyawa take yi, kuma su ma vata gari canza salo da dabaru suke yi.

Daga cikin matakan da ya kamata a bi wajen magance matsalolin tsaro a Nijeriya sun haɗa da daƙile cin hanci da rashawa. Domin kuwa cin hanci da rashawa babbar hanya ce ta maganin matsalolin Nijeriya, tun daga kan shugabanni har zuwa ga talakawa.

Sannan wajibi ne a ƙarfafa tare da inganta hanyoyin tattara bayanan sirri, saboda gano irin maƙarƙashiyar da wasu vata gari daga ciki da wajen ƙasar nan suke ƙoƙarin haddasawa ta hanyar amfani da wasu baragurbin ’yan ƙasa suna haifar da yamutsi nan da can, domin karkatar da tunanin hukumomi da jami’an tsaro wajen kunna wutar futintinun da ba za a gano tushen su da wuri ba, ballantana a samar da mafita. Matuƙar aka yi qoqari aka toshe wannan hanya to, lallai akwai kyakkyawan zaton za a samu sauƙin taɓarɓarewar gsaro a ƙasar nan.

Haka kuma har wa yau daga ɓangaren yadda jami’an tsaro ke amfani da ’yan jarida da kafofin sadarwa na zamani wajen yaɗa farfaganda da kururuta ayyukan da suke gudanarwa, don jawo ra’ayin jama’ar ƙasa. Hakan yana da muhimmanci, amma kuma yana da haɗari. Magance matsalolin tsaro tana da buƙatar sirri ne sosai da Kuma ƙwararrun ma’aikatan tsaro da sabbin dabaru.

Abin nufi a nan shi ne, dukkan wani aiki da aka shirya za a gabatar da shi bai kamata a yi ta yaɗawa a kafafen sada zumunta ba, saboda fitar da wannan sirri zai sanya waɗanda za a kai wa samame ko farmaki, su su sake sabon shiri. Amma matuƙar aka bar Al’amarin a cikin Sirri haƙina suna masu sakankancewa za a ci galaba a kansu. Babu shakka wannan ma hanya ce mai ɓullewa wajen magance matsalar tsaro.

Bisa la’akari da yawan jama’a da Allah ya albarkaci ƙasar nan da shi, ya zama tilas ga hukumomi su magance wannan matsala, wajen samar da guraben ayyukan yi, domin ɗauke tunanin matasa daga shiga ayyukan da ba su kamata ba.

Yana da kyau wajen ɗaukar ma’aikatan tsaro a tantance waɗanda suke da kishin ƙasa kuma ba a san su da mummunan halayya ba, ba wai kawai a dinga ɗiban yara ƙara zube ko waɗanda ke da gata da ɗaurin gindin manyan qasa ba, waɗanda babu abin da za su iya yi wa kansu sai sharholiya, da ƙara ɓata ƙasa.

Daga ƙarshe muna fatan Allah ya tabbatar mana da tsaro a ƙasarmu Nijeriya, ya kuma bamu lafiya da zaman lafiya baki ɗaya.

Daga Mannubiyya Abdulqadir Mu’azu, wata marubuciya da ke zaune a Jos, Jihar Filato, [email protected]

By Editor