Assalamu alaikum. Haƙiƙa ba ƙaramin tashin hankali ba ne, a ce an wayi gari matashi ba ya da takamaiman wurin da zai je domin neman na kansa. Rashin hakan ne ke sa ɗimbin matasa aukawa cikin miyagun ayyuka irin su; sace-sace da shaye-shaye da bangar siyasa da sauransu.
A wani ɓangaren ma sana’a ta fi muhimmanci fiye da wani ilimin, dalili shi ne sau tari matasa da yawa masu ilimi sukan yi amfani da iliminsu ta hanyoyin da ba su dace ba, sakamakon rashin sana’a inda wani lokacin ma ba za ka iya bambance matashi mai ilimi da marar ilimi ba, kamar wajen shaye-shaye da sace-sace inda dukansu sukan shiga riga iri ɗaya.
Saboda haka nake kira ga ’yan uwana matasa, masu karatu da marasa karatu cewa, mu fantsama ga harkokin kasuwanci domin neman halal ɗinmu da taimakon kanmu da iyayenmu, maimakon ci gaba da zaman muna jira daga wajen gwamnati ko iyayenmu. Lokaci ya yi da za mu farka daga dogon barcin da muke.
Ta yaya za mu fara kasuwanci?
Wannan tambaya ce mai ma’ana ganin cewa akwai sana’o’i da yawa waɗanda gurbatattu ne. To amma a nan muna magana ce a kan sana’o’i na halal musamman waɗanda muka gada daga wajen iyaye da kakanni.
Misali akwai, noma da ɗinki da fatauci da sauransu. Akwai kuma na zamani waɗanda yanzu su ma za mu kira su da sana’a domin ta nan mutane da yawa suke cin abinci, kamar kasuwancin Intanet da kayan shago da ɗaukar hoto da wankin mota da ginin zamani da kabu-kabu da sauransu.
Kaɗan daga cikin sana’o’in da na lissafo, wasu suna buƙatar jari don farawa, wasu da yawa a cikinsu kuma kawai biyayya da neman izini suke buƙata daga wajen iyayen gida masu yin irin wannan sana’a don farawa a matsayin yaro kafin kai ma ka koya a kai ga lokacin da kai ma za ka buɗe naka wajen sana’ar ko kasuwancin tare da janyo waɗansu yaran don koya musu. Amma fa duk hakan zai faru ne in an yi haƙuri. Allah Ya sa mu dace, Ilahee Ameen.
Daga Injiniya Mustapha Musa Muhammad. 08168716583.
