‘Ki faɗa wa Shugaban Ƙasa akwai yunwa a ƙasa’ – Cewar Sarkin Kano ga Uwargidan Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya buƙaci matar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, da ta isar da saƙon talakawa ga Shugaban Ƙasa dangane da yunwar da ake fuskanta a ƙasa saboda tsadar rayuwa, yana mai cewa wahalar da ake sha ta yi yawa.

Basaraken ya bayyana haka ne a lokacin da Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kai masa ziyara a ranar Litinin a fadarsa.

MANHAJA ta kalato cewar, Oluremi ta ziyarci Kano ne domin halartar ƙaddamar da ginin Sashen Nazarin Doka a Jami’ar Maryam Abacha wanda aka yi wa ginin laƙabi da sunanta.

Sarkin Kano ya ce, “Duk da dai akwai hanyoyi da dama na isar da saƙo ga gwamnati dangane da buƙatunmu, sai dai isar da saƙon ta hannunki ya fi sauƙi da zama tabbas wajen sanar da Shugaban Ƙasa halin da ƙasa ke ciki.

“Duk da dai ba a wannan gwamnatin aka fara ba, amma halin yunwa da walahar da ƙasa ke ciki abin damuwa ne ainun kuma mai buƙatar a ɗauki matakin gaggawa don magance shi.”

Basaraken ya ƙara da cewa, “Wata babbar matsalar da ake fuskanta har wa yau, shi ne rashin tsaro. Na san cewa gwamnatinku gado ta yi, amma ya kamata a yi wani abu domin kawar da waɗannan ƙalubalan.

“Muna samun tarin saƙonni daga wajen jama’a, ciki har da batun ɗage CBN da FAAN zuwa Legas, ina ganin ya kamata gwamnati ta fito ta yi wa ‘yan ƙasa bayani kan wannan batu da harshen da za su fahimta.

Gobara ta kama ofishin ‘yan sanda a Kano

Jaruma Fatima Sa’id ta kwanta dama

“A wayar da kan jama’a sosai kan batun. Ni kaina ba zan iya faɗin ainihin dalilin gwamanati kan batun ba, ya kamata a fahimtar da mu dalilin da ya sa gwamnati ke son ɗauke CBN da FAAN zuwa Legas ba.”

Daga cikin ‘yan tawagar da suka yi Oluremi rakiya yayin ziyarar, har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, Ƙaramar Ministar Abuja, Mariya Mahmoud Bunkure da dai sauransu.