Jaruma Fatima Sa’id ta kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa jaruma Fatima Sa’id Abdullahi da aka fi sani da Bintu a cikin shirin Ɗaɗin Kowa, rasuwa.

Jarumi Abba El-Mustafa ne ya bayyana rasuwar jarumar a shafukansa na sada zumunta a ranar Lahadi.

Nijeriya ta gaza lashe Kofin AFCON 2023

Shugabancin MOPPAN: Yadda Barde ya zama magajin Sarari a Kannywood

Sai dai babu wani karin haske kan abin da ya yi ajalin marigayiyar.

Masoyan marigayiyar daga sassa daban-daban na ci gaba da nuna alhininsu dangane da rasuwar jarumar.