Hedikwatar tsaro ta gargaɗi ƙungiyar HURIWA kan rikicin Filato

Daga WAKILINMU

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya, ta ja hankalin ƙungiyoyi masu ƙoƙarin ta’azzara al’amura a daidai lokacin da sojojin suke iya bakin ƙoƙarinsu dangane da samar da zaman lafiya yankin da ke fama da rikici a Jihar Filato.

Wannan dai na ɗauke a cikin wata sanarwa da hedikwatar ta fitar mai sa hannun darektan yaɗa labaranta, Burgediya Janar Tukur Gusau ranar Litinin ɗin nan a Abuja.

Birgediya General Gusau dai ya maryar da martani ne ga ƙungiyar HURIWA ta marubuta masu rajin kare haƙƙin bil’adama wadda ta soki kwamitin da aka kafa domin samo bakin zaren rikicin da ya dabaibaye yankin na jihar Filato.

Jaruma Fatima Sa’id ta kwanta dama

Kotu ta bai wa gwamnatin Tinubu umarnin daidaita farashin kayayyaki cikin mako guda

Ya ce kwamitin wanda babban hafsan sojojin ƙasar ya kafa da kansa na ƙarƙashin jagorancin tsohon babban soja mai tarin kwarewa.

Ƙungiyar ta HURIWA dai a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi ta hannun shugabanta na ƙasa, Emmanuel Onwubiko, ta soki babban hafsan sojin ƙasar inda ta ce ba da gaske yake yi ba wajen warware rikicin na jihar Filato.