Kotu ta bai wa gwamnatin Tinubu umarnin daidaita farashin kayayyaki cikin mako guda

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Ikoyi, Jihar Legas ce ta ba da wannan umarni a ranar Laraba, 7 ga Fabrairu.

Umarnin Kotun ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta daidaita farashin fetur da na saura kayayyaki a cikin mako daya.

Mai Shari’a Ambose Lewis-Allagoa ne ya ba da wannan umarni biyo bayan karar da Babban Lauyan Nijeriya kuam mai rajin kare hakkin dan’adam, Femi Falana SAN ya shigar Kotun.

A cewar Alkalin, “Na ji mai karar Femi Falana a cikin kararsa mai lamba FHC/L/CS/869/2023 kuma na gano duk da karar da aka shigar kan masu kare kansu, Atoni-Janar da Hukumar Kula da Farashi babu wata hammaya da aka samu dangane da haka, wanda haka doka ce cewa an amince da dukkan hujjojin da aka gabatar.”

Alkalin ya bukaci Gwamnatin Nijeriya da ta daidaita farashin madara, sikari, gishiri, keken hauwa, babur, fetur, gas, kananzir da sauransu.