‘Yan bindigar da suka sace ‘yan rakiyar amarya 63 a Katsina sun saki bidiyo

Daga UMAR GARBA a Katsina

‘Yan bindigar da suka sace mutane 63 dake kan hanyarsu ta kai amarya gidan mijinta sun saki bidiyo inda suka nuna fuskokin wadanda ake garkuwar da su.

Abubuwan da bidiyon ya kunsa shi ne, ‘yan bindigar sun fara kalubalantar jami’an tsaro inda suka bayyana cewa idan akwai wanda zai iya karbar mutanen ya zo ya jaraba, ya ga abun da zai faru da shi.

Sun kuma bayyana cewar idan ba a fanshi amaryar ba kan lokaci za su sake aurar da ita ga wani mijin.

A cikin bidiyoyin wadda yanzu haka ta karade safukan sada zumunta an ga yadda ‘yan ta’addar suka rataya wa matan bindigogi, a yayin da su kuma matan da ake tsare da su ke yin kira ga ‘yan uwa da abokan arziki a kan a kawo wa barayin kudi don a sake su.

Idan za a iya tunawa Manhaja ta rawaito yadda ‘yan bindigar suka yi wa motar dake dauke da ‘yan rakiyar amaryar kwanton vauna a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, suka kuma yi awon gaba da mutanen wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace mutane 35 ne aka sace.

Sai dai a cikin bidiyon ‘yan bindigar sun musanta inda suka ce, mutane 63 ne suke tsare da su a halin yanzu.

Har zuwa hada wannan rahotan rundunar ‘yan sanda ba ta mayar da martani kan faifain bidiyoyin ba wanda mutane ke ci gaba da tattauna a kan shi musamman a kafafen soshiyal midiya.

Ga wani bangare na bidiyon kamar haka: