Manomi ya yi wa Gwamna Bago kyautar doya don yaba ƙoƙarinsa

Daga BASHIR ISAH

Wani manomi a Jihar Neja ya yi wa Gwamnan Jihar, Umaru Mohammed Bago, kyautar luka-lukan doya domin yaba masa da kuma nuna farin cikinsa game da aikin cigaban al’umma da ke gudana a jihar.  

Da yake zantawa da shafin Tsalle Daya, Abdullahi Umar ya ce bayan da ya shigo garin Minna, babban birnin jihar ya ga irin ayyukan da Bago ke yi, hakan ya sa ya ga dacewar shirya masa wannan kyauta domin yaba kokarinsa.

Mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin siyasa da tsare-tsare, Nma Kolo ne ya karbi doyar a madadin Gwamnan, inda ya nuna farinciki tare da ba shi tabbacin sakonsa zai isa ga Gwamna yadda ya kamata.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar jihar Neja ke kokawa dangane da tsadar kayayyaki musamman na abinci a jihar wanda a cewarsu, hakan ya haifar da matsin rayuwa.

Idan dai za a iya tunawa, MANHAJA ta rawaito yadda kwanan nan wasu al’ummar Minna suka gudanar da zanga-zanga saboda tsadar rayuwa, lamarin da Gwamnan Bago ya bayyana da shirin wasu bata-gari masu neman daburta zaman lafiyar al’umma.