NAPPS ta buƙaci Gwamnatin Katsina ta sassauta haraji

Daga WAKILINMU

Kungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu, watau National Association of Proprietors of Private Schools (NAPPS) reshen jihar Katsina ta roki Gwamnatin jihar Katsina ta rage yawan harajin da hukumomi ke amsa wurin makarantu masu zaman kansu.

Shugaban kungiyar Alhaji Mansur Sani Jibia ne ya yi wannan kiran a yayin wani taro da kungiyar ta shirya kuma ta gayyaci masu ruwa da tsaki.

Katsina Post ta ruwaito cewa, hukumomin da kungiyar ta gayyata sun hada da hukumar tara kudaden shiga (IRS), sai kuma ma’aikatar ciniki da masana’antu.

Shugaban kungiyar ya koka akan yadda membobin kungiyar ke fuskantar matsi lamba wajen biyan haraji a lokutta daban daban daga hukumomin duk da halin da ake ciki.

Ya nemi hukumomin da su yi ma kungiyar bayani akan ire-iren harajin da kuma wanda ya kamata membobin su biya a saukake.

Alhaji Mansur Jibia ya bayyana cewa membobin kungiyar a shirye suke su biya kowanne haraji bayan sun samu gamsassun bayani daga hukumomin.

Hakan nan shugaban, a madadin membobin kungiyar ya roki Gwamnatin jihar da ta kalli halin da makarantu masu zaman kansu ke ciki da kuma gudunmawar da suke badawa ga cigaban ilimi a jihar.

Sannan yayi fatan cewa zaman zai warware dukkannin matsalolin da membobin ke fuskanta ta fuskar biyan haraji.

Da yake jawabi, shugaban hukumar IRS Alhaji Muhammad Isiyaku ya gode ma kungiyar bisa tunanin da tayi na shirya taron.

Shugaban hukumar yayi dogon jawabi akan kokarin hukumar na ganin ta inganta hanyoyin tara kudaden shiga tare da kirkiro sabbin dabaru a fadin jihar.

Sannan ya tabbatar da cewa a yanzu haka hukumar ta shirya daukar alhakin amsar haraji da kudaden shiga a fadin jihar kamar yadda doka ta tanada.

Ya tabbatar ma kungiyar da cewa hukumar za ta duba akan dukkanin korafe-korafen da kungiyar ta gabatar da duba yiwuwar gyara akan lamarin.

A yayin taron an shafe lokaci ana tattaunawa tare da kara ma juna sani akan hanyoyin biyan harajin da kuma korafe-korafen membobin kungiyar.

An shirya taron a babban dakin taro na Makarantar Koyon Aikin Kiwon Lafiya ta KEBRAM da ke cikin garin Katsina.