Ta haifi ’yan huɗu yayin yi wa ƙasa hidima

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata ’yar Nijeriya, wadda a halin yanzu take tsaka da yi wa kasa hidima (NYSC) ta haifi ’ya’ya hudu a yayin yi wa kasa hidima.

Wani faifan bidiyo da ke zagayawa a yanar gizo an yi masa taken, “Haihuwar ‘ya’ya hudu yayin hidima” kuma ya nuna matashiyar sanye da kakin NYSC.

A cikin faifan bidiyon, mahaifiyar da ke tsaye kusa da wani mutum-mutumi a sakatariyar NYSC, cikinta ya bayyana da girma.

A cikin shirin na biye, matar ta matsa kusa da kyamarar, ta bayyana fuskarta. Bidiyon ya nuna fuskokin jarirai hudu da ta haifa.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi tururuwa zuwa sashin sharhi don mika saqon taya murna ga wannan abin farin ciki.