Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
A karon farko da aka gudanar da auren mutane dari uku a fadar Mai Girma Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar a karkashin wata kungiya mai suna NANAS da matar gwamnan jihar Kebbi Hajiya Nafisa Nasiru Idris ke jagoranta.
Shi dai wannan auren sabanin irin aure-aure ne da aka saba shiryawa ba kamar na marayu ko zawarawa ba, wannan auren aure ne na marasa galihu irin wadanda ake saka rana ana dagawa saboda rashin abin auren ko kuma rashin abinda za a yi wa amarya kayan daki daga bangaren iyayen mace wanda ya kunshi yammata da zawarawa yayin da wadansu sun kara yin auren ne.
Shi dai wannan auren an zaqulo mutanen ne daga kowane bangare daga kananan hukumomi ashirin da daya da ke fadin jihar kamar yadda daya da cikin ’yan kwamitin auren daga karamar hukumar mulki ta Argungu ya bayyana.
Babban Shehin Malamin Addinin Musulunci Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shi ne ya jagoranci wannan auren na mutane 300 da suka hada da Marayu, Marasa Karfi da zawarawa.
Bayan an tantance kowane Ango da Amarya ta hanyar duba lafiyar su tun kwanan baya, Shehin Malamin bisa ga umurnin Maimartaba Sarkin Gwandu ya bada damar a biya Sadaki kan Naira Dubu Saba’in (₦70,000) ga kowace Amarya, nan take aka bada damar ƙulla aure kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.
Kowace Amarya ta sami gado, Kujeru, buhun shinkafa 25kg, Man gyada, Kuloli, murhu da dai sauran kayayyakin aikin gida da na girki.
Haka-zalika, a vangaren maza kuma kowane Ango an ba shi shadda yadi goma (10) da kudin dinki naira dubu biyar.
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Kebbi, Honarabul Usman Mohammed Ankwai shi ne ya wakilci Maigirma Gwamna Dr Nasir Idris (Kauran Gwandu).
Mai girma Matar Gwamnan Kebbi Haj Nafisa Nasir Idris Kauran Gwandu da matar Mataimakin Gwamnan Kebbi Haj Maryam Umar Abubakar Tafidan Kabi da tawagar su duka sun halarci wannan bukin auren.
Haka-zalika bukin auren ya sami halartar manyan malaman addini, sarakunan gargajiya, yanmajalisar dokoki, ma’aikatan gwamnati, yankasuwa da yansiysa.
Bayan kammala auren an gabatar da nasihohi ga ma’auratan na zamantakewa daga malamai daban-daban.
