Daga BASHIR ISAH
Wasu jami’an hukumomin tattara bayana asirri na kasa sun bankado shirin da wasu makirai ke yi na neman gwara kan sanatocin Arewa a Majalisar Tarayya da talakawansu.
Jami’an wadanda suka bukaci a sakaya sunansu su shaida wa jaridar PRNigeria cewa har wa yau, shirin na da nufin gwara kan hukumomin tsaron kasar nan don su rika ganin laifin juna game da matsalar tsaron kasa.
Sun bayyana hakan ne a matsayin martani a kan wani rahoto wanda ya yi zargin hukumomin tsaron sun kafa idanunsu kan wani Sanatan Arewa saboda zarginsa da ake yi da daukar nauyin ta’addanci, fashin daji da satar mutane.
A cerwar rahoton, an gano wani dan majalisa wanda ke jagorantar wani muhimmin kwamiti a Majalisar Dattawa a matsayin daya daga cikin masu daukar nauyin ta’addanci a yankin Arewa.
Sai dai, sa’ilin da yake martani kan wannan rahoto, wani babban jami’in tattara bayanan sirri ya tabbatar wa PRNigeria an gano wadanda ke da hannu a wannan rahoto wanda ya bayyana a matsayin kazon kurege.
Ya ce, “Bincikenmu ya bankado wadanda ke daukar nauyin yada labarin karya a kafafen yada labarai.
“A halin da ake cike, babu wani sanata da muke bincike a kansa dangane da batun daukar nauyin ta’addanci ko fashin daji.”
Jaridar News Point Nigeria ta rawaito shi ma babban jami’in soji wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sun bankado wadanda ake zargi da kirkirar rahoton karyar da aka yada da nufin taba mutuncin sanastocin Arewa.
Ya kara da cewa, “Yayin bincikenmu mun gano wani soja da ya yi ritaya amma aka ba shi damar ci gaba da aiki, shi ne jigo wajen kirkirar rahoton. Kuma tsohon jami’in ya fito ne daga wata jiha a tsakiyar Nijeriya.
“Amma duk lokacin da kuma dafa shi, za a sa shi ya bayyana Sanatan da yake zargi. Domin ba daidai ne ba ka gwara kan wasu ‘yan tsiraru da na al’ummar Nijeriya ba.”
