Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Batun satar mutane ana garkuwa da su don neman kuɗin fansa ba sabon abu ba ne, musamman ga yara mata, ko ɗaliban makarantu da sauransu. Sai dai wani sabon salo da gungun waɗannan ɓatagari suka ɓullo da shi shi ne satar ‘yan mata a cikin birnin Abuja.
Na san kuna da labarin ‘yan matan nan su biyar da aka yi garkuwa da su, har ma aka kashe wata daga ciki, mai suna Nabeeha. Waɗanda ba a jima da karɓo fansar su ba.
Sai kuma ga shi da safiyar ranar Laraba da ta gabata an samu labarin wani gungun ’yan bindiga su shida da suka shiga wata anguwa a Kubwa, cikin yankin Bwari a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da wasu yara mata su 2 da namiji ɗaya, duka ‘ya’yan mutum ɗaya. Rahotanni sun bayyana cewa matan ba su wuce ‘yan shekara 14 da 16 ba.
Sai dai shi namijin da suka tafi da shi, sun sako shi ya kawo saƙo gida, cewa sai an biya Naira Miliyan 30, kafin a saki sauran ‘yan uwan nasa.
Wani abin takaici ma shi ne, ɗaya daga cikin yaran matan daga barci ta tashi, babu kaya a jikinta sai rigar barci. An ce mahaifiyar yaran ta yi ta roƙon su don su bar yarinyar ta sa kaya, saboda sanyi amma suka hantareta.
Wannan yana zuwa ne bayan da wasu ’yan bindiga suka sako sauran ’yan mata huɗu daga cikin biyar ɗin da suka yi garkuwa da su tare da mahaifinsu Alhaji Mansoor Alqadriyar tsawon kwanaki 18, waɗanda aka sace daga gidansu da ke Zuma yanki na farko a Bwari da ke Abuja.
Yayin da suka sake mahaifin yaran bayan kwana uku yana hannunsu, bisa buƙatar ya je ya nemo kuɗin fansar ’ya’yansa. Sai dai sakamakon jinkirin da aka samu na kasa haɗa kuɗin a wa’adin da ’yan bindigar suka bayar sun yi wa ɗaya daga cikin yan matan mai suna Nabeeha kisan gilla. Lamarin da ya girgiza ’yan Nijeriya da dama.
Idan ba mu manta ba, wani gungun ‘yan bindiga ne suka kama ‘yan matan su biyar tare da mahaifinsu a farkon watan Janairu da ya gabata, inda suka nemi kuɗin fansa Naira Miliyan 10 kan kowannensu, wanda jimilla ya zama Naira Miliyan 60. Sai dai bayan da aka gagara biyan kuɗin fansar a kan lokaci, waɗannan mugayen mutane sun ƙara yawan adadin kuɗin zuwa Miliyan 100. Sannan kuma suka ƙara barazanar kashe wasu daga cikin yaran, idan har aka gaza biyansu kuɗin fansar.
Sai da ta kai ga ’yan Nijeriya sun yi musu karo-karo wajen haɗa kuɗin kafin ya kai adadin abin da ’yan bindigar suka nema a basu. Madalla da gudunmawar da tsohon Ministan Fasahar Sadarwa Dr Isa Ali Pantami, wanda ya yi hanyar samun wani kaso mai tsoka na tallafin kuɗin daga wajen wani bawan Allah, da ya bayar da Naira Miliyan 50.
Kodayake ba a bayyana nawa aka biya domin sakin ’yan matan ba, amma wani ɗan uwan mahaifinsu ya shaidawa manema labarai cewa, an sako ’yan matan ne tare da wasu mutane su takwas, waɗanda su ma aka yi garkuwa da su, a lokuta da wurare daban-daban. Amma ’yan bindigar sun nemi a haɗa kuɗin fansar ne duka a waje guda a kai musu, inda suka bayyana wanda za a bai wa kuɗin ya kai. Saɓanin rahoton da jami’an ’yan sanda suka fitar kan cewa su ne suka kuɓutar da ’yan matan, bayan fafatawa da ’yan bindigar.
Ko ma dai ta yaya aka kuvutar da waɗannan ’yan mata, abin dubawa da nazari a nan shi ne har yaushe wannan al’amari ya zamo haka a tsakanin mu. Rayuwar mu ta zama abin farauta, ana cikin rai da ’yancin ɗan adam kamar tumatir a kasuwa. Allah Ya kyauta.
Na taɓa jin yadda tattaunawar wani da aka ɗauke ɗan uwansa yake ciniki da wani ɗan bindiga kan abin da za a bayar a fanshi wanda aka yi garkuwa da shi. Akwai tsoro da firgici sosai a yadda wannan al’amari yake kasancewa.
Tun a shekarar 2014 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace wasu ’yan mata su 276 daga makarantar kwana ta garin Chibok a Jihar Borno, garkuwa da ’yan mata da ’yan makaranta ya zama abin ya yi a tsakanin ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, saboda kuɗaɗen da suke samu masu ɗimbin yawa, da yadda hankalin hukumomi da iyaye ke tashi a kai.
A wani bincike da wata jaridar ƙasar Amurka ta gudanar, an ƙiyasta cewa a cikin shekarar 2023 kowacce rana ana ɗauke mutane 45 akasarin su ’yan mata. Dubban mutane ake yin garkuwa da su a Nijeriya tare da biyan miliyoyin Naira don fansar waɗanda aka sace.
Yayin da harkar garkuwa da ’yan mata ta zama babbar harka da ke kawo maƙudan kuɗaɗe cikin ƙanƙanin lokaci. Abin da ya mayar da manyan ayyukan laifi irin su fashi da makami a kan hanyoyi, fashin bankuna da fasa gidaje domin satar kuɗaɗe da dukiyoyi ya zama tsohon ya yi.
Ba za mu ce jami’an tsaron Nijeriya ba sa yin ƙoƙari wajen yaƙi da waɗannan batagari ba, tun da muna ganin yadda suke kai hare-hare, da kai samame wuraren da suke ɓoye a dazuka da cikin gari, amma duk da haka akwai buƙatar ƙara ƙaimi da fitar da sabbin dabaru na yadda za a yi yaƙi da waɗannan ’yan bindiga.
Ko a kwanakin nan ma mun ga rahoton yadda jami’an ’yan sanda suka kama wani ɗan bindiga mai suna Bello Mohammed ɗan asalin Jihar Zamfara, a wani otel a garin Tafa da ke yankin Jihar Kaduna, kuma har ya amsa yana daga cikin gungun ’yan bindigar da suka sace ’yan uwan Nabeeha.
Muna fatan jami’an tsaro, na sojoji da sauran rundunonin tsaro za su cigaba da haɗa gwiwa wajen aiki da jama’a don samun rahotannin sirri na yadda za a daqile waɗannan ayyuka na cin zarafin ɗan adam, da cutar da rayuwar ’ya’yanmu mata iyayen al’umma.
Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan fitina da tona asirin mugayen mutanen da suke aikata wannan ta’addanci, a sassan ƙasar nan, suna vata sunan ’yan Arewa da ƙabilar Fulani. Kodayake ba duk masu aikata wannan ta’asa ne Fulani ba, akwai sauran ƙabilu da ke fakewa da ayyukan ’yan bindiga, suna aikata nasu ta’addanci.
Ya Allah ka yi mana maganinsu.
