Daga BASHIR ISAH
A ranar Lahadi aka kammala Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) na 2023 inda aka ɓarje gumi tsakanin Nijeriya da Ivory Coast a wasan ƙarshe.
A ƙarshe, Ivory Coast ce ta zo ta ɗaya a gasar bayan da ta doke Najeriya da ci 2 da 1 a wasan ƙarshe na gasar.
Mai masaukin bakin ta zama zakara ne, bayan ta warware ƙwallon da Nijeriya ta jefa mata kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Shettima ya taya Super Eagles murnar shiga zagayen karshe a garsa AFCON 2023
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Ivory Coast ta warware ƙwallon a minti na 62 daga hannun ɗan wasan tsakiyarta, Franck Kessie.
A minti na 81 Sebastian Haller ya ƙara wa mai masaukin baƙi ƙwallo ta biyu a raga, wanda hakan ya sanya ta zama zakarar AFCON ta 2023 a inda Nijeriya ta zo ta biyu.
