Shettima ya taya Super Eagles murnar shiga zagayen karshe a garsa AFCON 2023

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya taya ’yan wasan Super Eagles murnar samun nasarar kaiwa zagayen karsahe a gasar AFCON 2023 da ke gudana a Ivory Coast.

‘Yan wasan Super Eagles na Nijeriya sun taki wannan nasarar ce bayan da suka yi galaba a kan ‘yan wasan Bafana Bafana na Afirka ta Kudu a wasan da suka buga ranar Laraba a filin Stade de la Paix da ke Bouake.

An kare wasan ne da 1-1 bayan shafe mintoci sama da 100, wanda a karshe wasan ya kammala da bugun fenariti.

Yanzu dai tun da ta samu tsallake siradi zuwa zagayen karshe, Nijeriya za ta buga wasanta na karshe ne walau da mai masaukin baki, wato Ivory Coast ko kuma Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya zuwa ranar Lahadi.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ne ya tura mataimakin nasa zuwa Ivory Coast domin kara wa ‘yan wasan Nijeriya kwarin gwiwa a gasar.