Mutane na girmama ni saboda lashe gasar Hikayata – Aisha Fulani

“Zumuncin marubuta abin a yaba ne sosai”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Aisha Abdullahi Yabo ba bakuwa ba ce a cikin marubuta, musamman marubutan onlayin, inda take daya daga cikin masu ba da gagarumar gudunmawa ga cigaban adabin Hausa. Ita ce ta zo gwarzuwa ta biyu a Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2023. ‘Ya ce ga fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Zamfara, Sheikh Abdullahi Abubakar Yabo. Don haka babu mamaki jin cewa, Aisha da aka fi sani da Fulani, hafizar Alkur’ani Mai Girma ce, kuma masaniya a sauran fannonin ilimin addini, kuma har yanzu tana cigaba da neman ilimi. Yanzu haka ita ce Mataimakiyar Shugaban sabuwar kungiyar Marubutan Jihar Zamfara, (ZAMWA). A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana abin da ya fara sa ta shiga harkar rubutun adabi, da kuma yadda take samun girmamawa daga wajen jama’a bayan nasarar da ta samu a gasar Hikayata. Ga yadda cikakkiyar hirar tasu ta kasance. 

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki? 

FULANI: Sunana Aisha Abdullahi Yabo, wacce a ka fi sani da Aisha Fulani. Ni marubuciya ce kuma daliba. Ni ce kuma Maitamakiyar Shugaban Kungiyar Marubutan Jihar Zamfara wato Zamfara Writers Association (ZAMWA). Ina da yara huɗu, duka maza, amma Allah Ya yi wa ɗaya rasuwa a kwanan baya. 

Ko za ki ba mu tarihin rayuwarki?

Ni ‘yar Jihar Zamfara ce daga garin Gusau. Na taso ne a gidan ilimi da malanta, ban samu shiga makarantar boko ba, amma na yi karatun allo da wasu littattafan addini a Zawiyyar Shehu Balarabe Gusau.

Mene ne alakarki da Jihar Sakkwato, wasu na cewa ke ƴar Sakkwato ce. Yaya gaskiyar abin yake? 

E, haka ne. Asalin mahaifana ‘yan Jihar Sakkwato ne, daga wani qauye da ake kira Ruggar Mallam wanda yake cikin Karamar Hukumar Yabo. Karatun almajiranci ne ya kawo mahaifina Zamfara a cikin garin Gusau, inda ya zauna a Zawiyyar Shaihu Balarabe. A nan ya zauna zaman almajiranci har ya yi aure ya kafa iyalinsa. Ni ce babbar ƴarsa, kuma tare da sauran ƴan’uwana mu 19 duk a nan Gusau aka haife mu. Maza 10, mata kuma 9.

A lokacin tasowarki wadanne abubuwa ne suka faru da ke wanda suka taimaka wajen karfafa miki gwiwa a rayuwa?

Abubuwa da yawa sun faru a rayuwata da ba lallai na iya fadar su kai tsaye ba, sai dai abin da zan iya cewa a cikin wannan rayuwar ne na fahimci menene haquri da kuma ribar da haquri yake da shi a cikin rayuwar ɗan’adam, uwa-uba kuma tasirin addu’a. Wadannan sune kwarin gwiwa a rayuwa.

A matsayinki ta wacce ta taso cikin gidan malamai, kasancewar mahaifinki fitaccen malamin addinin Musulunci ne, yaya tarbiyyar ki ta bambanta da na sauran yara?

E, tabbas mun taso cikin yanayi na tarbiyya da neman ilimi. Ba mu samu sake ko zarafin wasanni irin na sauran yara ba. Na taso a yanayi na ina za ki makaranta ina ki ka fito makaranta. Mu kan tashi tun da asuba, muna idar da sallah za mu tafi makaranta, sai karfe takwas saura muke fitowa. Abinci kawai za mu ci mu tafi Zawiyya sai sha biyun rana kuma za mu dawo. Idan har ranar biyawarmu ce to, muna dawowa rubutu za mu yi a allo, ana yin azahar abinci kawai za mu ci mu koma makaranta, karfe huɗu mu fito. Ana yin sallar La’asar za mu shiga Masa’iyya da take cikin gidanmu, sai karfe shida za a tashi. Bayan sallar Isha’i kuma za mu wuce zuwa makarantar dare. To, ko na so na yi wasa a cikin yara ‘yan’uwana babu wannan lokacin. Ranar Alhamis da Jumma’a ma da zarar mahaifinmu ya ji mun fiya surutu ko kiriniya yanzu zai kiramu dakinsa ya zaunar da mu ko mu yi karatu, ko kuma ya sa mu cika allo da rubutu. Fannin tarbiyya kuma bayan dora mu kan turbar karatu mun samu tarbiyya sosai daga mahaifanmu fannin addini da kuma zamantakewar rayuwa. Alhamdulillah, ina godiya ga Ubangiji a koyaushe da samun iyaye nagari masu tsayuwa kan tarbiyyarmu, ba mu kadai da suka haifa ba, har dubban al’umma. Alhamdulillah!

Gaya mana yadda ki ka fara sha’awar rubuce-rubucen Hausa, kuma wadanne marubuta ne ki ka fi son karanta littattafansu?

Gaskiya yawan karatun littatafan Hausa shi ne abin da ya janyo har na fara jin ina sha’awar ina ma ni ma zan iya, sai dai kuma ina jin kamar ba zan iya ba, musamman idan na tuna ni fa ban yi boko ba to, ta yaya zan ma iya! Hakan ya sa na hakura ba don wannan muradin ya bar zuciyata ba. Sai ga shi cikin hukuncin Ubangiji na tsinci kaina a cikin marubuta a matsayin marubucya. Gaskiya marubutan da na fi jin dadin bibiyar rubutunsu suna da yawa sai dai kaxan daga cikin su akwai Aunty Fauziya D. Sulaiman, da Aunty Maimuna Idiris Sani Beli, da kuma Aunty Umma Sulaiman Ƴan awaki (Aunty Baby), a maza marubuta kuwa akwai Muhammad Lawal Barista, sai Abdullahi Jibiril Larabi, da kuma Nazir Adam Salih, da Abdullahi Hassan Yarima.

Wanne jigo ne ya fi birge ki wajen karatun littafin adabi?

Ina son jigon da yake tavo soyayya da kuma zamantakewar aure. Wato irin labarin da yake tavo matsalolin gidan aure. 

Yaya ki ka samu kanki a matsayin marubuciya?

A lokacin da aka fara rubuta littattafan Hausa a onlayin ina bibiyar zaurukan marubuta ina karanta littattafan da ake dorawa. Watarana bisa kuskure na tura wani talla a wani zauren marubutan, wanda doka ne ba a tura wa. Bayan na tura na sauka ina dawowa na tarar da ta fitar da ni, da na bita ta akwatin sirrinta na tambayeta dalili sai ta ce saboda na yi talla ne. Na bata haquri akan rashin sani ne na kuma nemi alfarmar ta mayar da ni amma sam ta ki, hakan ya bata mini rai sosai. Sai kawai na ji ni ma ai idan nasa kaina zan iya. A ranar na buxe nawa zauren, kuma a ranar na fara nawa rubutun.

Wanne labari ki ka fara rubutawa, kuma wa ya taimaka miki wajen sanin yadda za yi?

Labarin da na fara rubutawa shi ne ‘Amal’, littafina na farko. Akwai wani Nafi’u wanda yake tura littattafan marubuta a zauruka, da ya ga na fitar da labarina a rarrabe, sai ya fada min yadda zan riqa yi a hade. Zan iya cewa shi ne farkon wanda ya fara nuna min yadda zan yi.

Akwai dan’uwana Sabir Salihu wanda shi ma ya ba ni gudunmawa a cikin rubutuna. Sai kuma babban malamina Almu Dakata wanda shi ne ya fara koyar da ni ka’idojin rubutu da yadda zan rarraba wasu kalmomi. Ba zan manta da taimakon da Malam Jibiril Rano yake ba ni ba, kasancewara babban jigo a wajen samun ilimin yadda zan inganta rubutuna ta fannin ka’idojin rubutu. Sai kuma Yaya Yusuf Gumel, shi ma ya matuqar taimaka min wajen koyar da ni da kuma ba ni shawarwarin yadda zan inganta rubutuna. 

Kawo yanzu kin rubuta littattafai nawa? Kawo sunayensu da bitar wasu fitattu uku daga ciki?

Na rubuta littattafai goma. Akwai ‘Amal’, ‘Mu Kula ‘Yan Matan Zamani, ‘Ma’aurata’, ‘Illar Auren Dole’, ‘Kar Ka Guje Ni’, ‘Su Ne Sila’, ‘Kuskuren Waye?’ ‘Mahaukaci Ne Ko Aljani?’ Sai ‘Fargar Jaji’, da kuma ‘Kasata’. 

Shi littafin Ma’aurata, yana dauke ne da labarin wasu iyalai biyu masu matsaloli mabambanta game da zamantakewar aure. Daya gidan mijin ya kasance dan giya manemin mata, ga kuma dukan mace, yayin da ita matarsa ta kasance mai hakuri da son addini da jurewa halinsa duk da kasancewar shi din ba zavinta ba ne. Daya gidan kuma mijin ya kasance mai addini da hakuri, sai dai ya yi rashin sa’ar mace tagari. Hakan ya sa ya kara aure sai dai ya yi gudun gara ne ya fada gidan zago kasancewar har gara matsalar uwargidan da matsalar amaryar da ta kasance tana da saurayi a waje, burinta ta kwashe kudinsa ta koma wa tsohon saurayinta.

Shi kuma Kuskuren Waye? Labari ne akan wasu kawaye da suka kasance tamkar ‘yan biyu, kasancewar komai nasu iri daya ne, tare suke yin komai. Namiji ne ya shigo tsakaninsu sanadin cin amanar da kawar ta yi mata a dalilin kuskuren da daya kawar ta aikata.

Akwai kuma littafin Fargar Jaji, wanda labari ne kan wata matashiya da ta biyewa romon bakan namiji da soyayyarsa ya sa ta yi saka da mugun zare, ta zabe shi ta bar mafarin zuwanta duniya, wato mahaifanta, ta bar kowa nata ta zabe shi a matsayin komai nata, hakan ya jefata a komar da-na-sani.

Wanne littafi ne a cikin littattafanki za ki ce shi ne ya fara fitar da sunanki a duniyar marubuta?

‘Ma’aurata’ shi ne littafin da ya fara fito da ni a duniyar rubutu. Labari ne da na gina shi akan wasu matsaloli da ma’aurata suke fuskanta bangaren mace da kuma bangaren namiji, a cikin labarin na fito da muhimmancin da haquri yake da shi da kuma addu’a wanda idan ka bar wa Allah komai sai ya ma mafita a lokacin ba ka yi zato ko tsammani ba. Sannan a labarin na nuna irin yadda sakamakon wanda ya ci amanar aure take bayyana tun a duniya.

Shin ke ma ki kan yi rubutu bisa wani abu da ya shafi rayuwarki ta zahiri, ko na wasu da ki ka sani kamar yadda wasu ke yi, ko kuma kina zama ne ki kirkiro da labarin?

Shi rubutu ai abinda yake faruwa ne dama marubuci zai dora alkalaminsa a kai, don haka duk wani labari da zan kirkira wajen yin rubutu abu ne da yake faruwa a cikin al’umma, sai dai kawai bambancin ban tava rubuta wani abu da ya shafi rayuwata ba, haka zalika rayuwar wani na kusa da ni, kirkirar labarina nake akan abin da na san yana faruwa a wannan duniyar da muke ciki.

Wadanne marubuta ne ki ke kallo a matsayin madubinki a fagen rubutun Hausa?

Allon dubana a rubutu, gaskiya su ne dai waɗanda na ambata a baya. Aunty Fauziya D. Sulaiman, Aunty Maimuna Idris Sani Beli, sai kuma Aunty Umma Sulaiman ‘Yan Awaki. Wadannan su ne maduban dubana a rubutu.

Kina daga cikin shugabannin sabuwar kungiyar Marubutan Jihar Zamfara, ko za ki gaya mana manufofin kafa kungiyar?

Manufofin kafa kungiyar su ne ganin mun haɗa kan marubutan Jihar Zamfara, mu cure waje ɗaya mu zama tsintsiya madaurinki ɗaya ta wajen kawo cigaban rubutunmu, ba da dama ga sababbin marubuta su shigo a hadu a taimaki juna wajen inganta adabin Hausa, da taimakawa marubutanmu masu taso wa. 

Wanne canji ku ke so ku kawo a rayuwar marubutan Zamfara?

A cikin canje-canjen da muke so mu kawo a rayuwar marubutan jiharmu ta Zamfara shi ne koyar da ka’idojin rubutu, domin inganta rubutunmu, da kuma koyar da tsarin shigar da littattafai a kasuwar yanar gizo cikin sauki. Fannin rubutun fim ma kar a bar mu a baya, haka nan ma a fagen rubutattun wakoki. Muna so mu ga marubutan Jihar Zamfara sun shiga sahun manyan kungiyoyin marubuta na jihohin Arewa, musamman wadanda suke maqwaftaka da mu ta fannin samun cigaba da kuma nasarori a fannin Adabin Hausa da sauransu.

Wanne kwarin gwiwa nasarar da ki ka samu na zama ta biyu a gasar Hikayata ta BBC Hausa ya kara miki a fagen rubutu?

Alhamdulillah! Samun nasarata a gasar Hikayata ta BBC Hausa gaskiya ya kara min wani kaimi wajen sake inganta rubutuna da son qara kutsawa cikin kowacce gasar rubutu ba tare da fargaba ba.

Wanne abu ne ya canza a rayuwarki tun bayan samun wannan nasara da ki ka yi?

Gaskiya, AlhamdulilLah zan iya cewa rayuwata ta sauya sosai daga lokacin da na zama daya daga cikin gwarazan Hikayata. Saboda na hadu da dimbin masoya waɗanda ban taba zaton samunsu ba. Mafi yawan fitar da nake yi sai a dinga nuna ni ana ce wa wannan ita ce wacce ta ci gasar nan ta BBC. Al’ummar da suke kewaye da ni koyaushe budar bakinsu Aisha, muna alfahari da ke. Idan ana taro ana ba da kwatance da ni da kowa ya zama mai jajircewa kamar Aisha ku duba ba ta yi boko ba, amma dubi inda ta kai a yanzu, da sauransu. Ina samun mutuntawa daga mutanen da ke gaba da ni ta fannin shekaru da ma sauran vangarorin rayuwa. Na shiga inda ban tava zaton zan kai ba saboda ina ga matsayina bai kai na shiga ba, duk a dalilin gasar, AlhamdulilLah.

Wacce shawara ki ke da ita ga sauran marubuta da ke sha’awar shiga wannan gasa?

Shawarata ga ‘yan’uwana marubuta masu niyyar shiga wannan gasar ita ce na farko su dage wajen yin rubutun gajerun labarai ba wai na gasa ba a’a a matsayin gwaji suna turawa masana ana duba musu da ba su shawarwari, hakan zai sa su goge sosai ko da za a bude gasar rubutun ba zai ba su wahala ba. Sannan su zama masu bibiyar labaran da suka yi nasara, hakan zai ba su dama fahimtar yadda za su dora nasu alqalamin ba tare da kwaikwayon wani ba. Sannan bayan rubuta gasar kar a yi gaggawar turawa a bai wa masana su duba da kuma neman shawara. Su kuma rika bitar labarin, hakan zai ba su damar ganin kurakurai suna gyarawa. Idan an tura kuma sai a dage da addu’a, domin ita ce nasarar ba iyawa ko kwarewa ba. Nasara ta Allah ce, a roke shi idan da rabo sai a ga an dace. 

Mene ne ya fi birgeki game da zumuncin da ke tsakanin marubuta?

Lamarin marubuta ba a cewa komai, saboda zan iya cewa ban ga wani abu na jama’a da ake curewa a zama daya tamkar uwa daya uba daya ba irin marubuta ba, idan abin farin ciki ya samu daya sai ka ga duka ana wa juna farinciki haka abin kuka idan ya zo tare za a yi kuka. Idan aka zo fannin neman taimako haka za a hadu a taimaki juna, marubuta an zama tamkar uwa daya uba daya. Zumuncin marubuta yana matukar burgeni ina jin su din wata duniya ce daban Allah Ya yi a matsayin abu daya.

Mene ne ki ke bukatar ba da shawara a kai, don inganta rayuwar marubuta?

Matuqar marubuci yana so ya yi karko a matsayinsa na marubuci, to ya zamo mai gaskiya. Idan na ce gaskiya ina nufin duk abin da za ka ɗora alkalami ka yi rubutu kanshi ka sa tsoron Allah a ciki ka rubuta abinda ka san ba za ka ji kunyar iyaye ‘ya’ya ko dangi su karanta ba, abinda ka san har a wajen Allah ba za ka zama mai laifi ba, abinda ka san zai zama mai gyara tarbiyya ba vata tarbiyya ba. Idan har muka tsarkake alqalaminmu in sha Allah rayuwarmu za ta zama ingantacciya.

Akwai wasu marubutan da suke bude zauruka a manhajar YouTube ko Facebook da WhatsApp don tallata littattafansu ke wanne tsarin ki ke amfani da shi.

Duka ina amfani da wadannan manhajojin WhatsApp da kuma Facebook da YouTube, har ma da wasu manhajojin kamar su Bakandamiya Hikaya. Ina da canel a manhajar YouTube mai dauke da sunana Aisha Abdullahi Yabo TV, inda ake karanta wasu littattafaina. 

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Mai hakuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romonsa.

Na gode.

Ni ma na gode.