Bai wa al’ummarmu tsaro ne babbar manufarmu – Gwamna Lawal

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jadda cewa, bai wa al’ummar jihar cikakken tsaro shi ne babbar manufar da gwamnatinsa ta sa gaba.

Lawal ya bayyana haka ne a wajen tsaron majalisar tsaron jihar da ya gudana a karkashin jagorancinsa  ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, babban birnin jihar.

Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Kakakin Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya ce samar da Dakarun Tsaron Al’umma na Jihar Zamfara da kaddamar da kwamitin kula da Asusun Tallafa wa Sha’anin Tsaro na daga cikin manyan batutuwan da taron ya tattauna.

Idris ya ce, Lawal ya bukaci a samu hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro a jihar domin samun nasara dangane da yaki da matsalar fashin daji a jihar.

A cewar Lawal, “Gwamnatin jihar ta kirkiro Dakarun Bai wa Al’umma Tsaro na Jihar Zamfara ne a bisa shawarwarinku. A makon da ya gabata zubin farko na dakaru 2,720 suka kammala karbar horo wanda kuma an tura su aiki a sassan kananan hukumomi 14 da jihar ke da su.

“An tanadi baki dayan kayan aikin da ake da bukata da suka hada da ofisoshi a yankunan kananan hukumomi 14. Akwai motocin aiki guda 15 da Hilux guda bibbiyu ga kowace karamar hukuma in ba da Gusau da Maru wanda suka samu motoci guda ashirin-ashirin da Hilux hurhudu” da dai sauransu, in ji Gwamna Lawal.