Tinubu ya bada umarnin gaggawa kan raba ton 100,000 na abinci ga ‘yan ƙasa

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani mataki na neman daƙile tsadar rayuwa da ƙarancin abincin da ‘yan ƙasa ke fuskanta, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa kan a saki kayan abinci har ton 100,000 don amfanin ‘yan ƙasa.

Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Bada Tallafin Abinci a ranar Alhamis.

Idris ya ce, gwamnati ta shirya shigo da abinci daga ƙetare domin cike giɓin da ka iya aukuwa bayan kammala raba kayan abincin.

Ya ƙara da cewa, yanayi na buƙatar gaggawa na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa domin tabbatar da wadatar abinci a sassan ƙasa.

Tun bayan da sabuwar gwamnatin ƙasar ta cire tallafin man fetur ne dai a watan Mayun 2023 ‘yan Nijeriya suka fara fuskantar tsadar rayuwa inda farashin kayayyakin masafuri ya yi cillawar da ba a taɓa ganin irin sa ba a ƙasar.