Nijeriya ce ƙasa mafi sauƙin rayuwa a Afirka – Fadar Shugaban Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ofishin Shugaban Nijeriya ya tayar da ƙura da iƙirarin da ya yi na cewa ƙasar ta fi ƙarancin tsadar rayuwa a nahiyar Afirka.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne ya faɗi hakan a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da yake yin watsi da sukar da Atiku Abubakar ya yi cewa manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu na ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin wahala.

Mista Onanuga ya bayyana wani nazari da wani kamfani intanet Numbeo ya yi kan matsayin Nijeriya a tsarin tsadar rayuwa.

Ya ce cibiyar tattara bayana ta Numbeo ta ce Nijeriya ce ke da maki mafi girma wajen samun araha.

Amma hakan ba ya cikin dukkan ƙasashe 54 na Afirka, domin ƙasashe 23 ne kawai a nahiyar aka gudanar da binciken a kansu.

Matsayin Nijeriyar zai iya yi wa ‘yan qasar daɗi kaɗan – waɗanda ke fama da hauhawar farashin kayayyakin abinci da kayan masarufi, da asarar tallafin man fetur, da kuma ƙarancin kuɗi.