Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya
A ranar Juma’ar da ta gabata Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya jagoranci buɗe masallacin juma’a a garin Fammadina a gundumar Dutsen Abba da ke Zariya.
Taron buɗe masallacin ya samu halartar wanda ya gina masallaci wato Alhaji Umar Faruq Suleiman da masana ilimin addinin Musulunci da kuma fitattun ‘yan siyasa da suke ciki da wajen jihar Kaduna.
Mai martaba Sarkin Zazzau a jawabinsa ya fara da addu’a ta musamman ga wanda ya gina masallacin a cikin lokaci ba mai tsawo ba.
Malam Ahmed Bamalli ya kuna matuƙar jin daɗinsa na yadda wanda ya gina masallacin ya sa ido, na ganin an yi gini mai inganci daga fara ginin masallacin zuwa kammalawa.
A dai jawabin mai martaba Sarkin Zazzau ya ce dole ya yaba wanda ya gina masallacin na yadda ya kashe maqudan kuɗaɗe wajen gina makarantar Islamiyya da kuma wajen alwalla da kuma kama ruwa, duk a harabar masallacin.
Mai martaba Sarkin Zazau ya kammala da kira ga al’ummar Fammadina da sauran garuruwa da su ke kewaye da wannan garin da su tabbatar sun rsya masallacin da ibada da kuma neman ilimi.
Tun farko wanda ya gina masallacin Alhaji Umar Faruq Suleiman ya gina wannan masallaci ne domin ci gaban addinin Musulunci a dalilin wani amininsa da ya bayyana ma sa buƙatun gina wannan masallaci da al’ummar suke da shi.
Alhaji Umar Suleiman ya lashi takobin yin gine-ginen azuzuwa a makarantar firamaren da ke wannan gari na Fammadina a cewarsa za a fara ginin ba tare da vata lokaci ba.
Ya kuma nuna matuƙar jin daɗinsa na yadda Mai martaba Sarkin Zazzau da kansa ya halarci buɗe masallacin, wannan a cewarsa ya ƙara ma sa ƙwarin gwiwar ci gaba da ciyar da musulunci da kuma musulmi gaba a duk inda ya tsinci kansa a nan gaba.
Shi ko babban limamin wannan masallaci kuma liimami Fammadina, Sheikh Imam Dauda Ibarahim da farko bayan ya gabatar da huɗubar Juma’a a sabon masallacin, sai kuma ya yi addu’a ta musamman ga Alhaji Umar Faruq Suleiman na yadda ya yi amfani da dukiyarsa ya gina wannan masallaci da makarantar Islamiyya a harabar masallacin.
Imam Dauda Ibrahim bayan ya nuna kuma godiyarsa ga Mai martaba Sarkin Zazzau da ya jagoranci buɗe masallacin, sai ya ce ya karvi umurnin mai martaba Sarkin Zazzau na raya wannan masallaci da ibada da kuma ilimi, kamar yadda ya bayar da umurni a lokakacin da ya gabatar da jawabinsa.
